Idan na daina zan mutu: Bidiyon matar da ta shekara 4 tana kwankwadar fitsarinta a madadin ruwa
- A cikin shekaru 4 da suka gabata, wata mata daga garin Colorado a kasar Amurka mai suna Carrie ta kamu da tsananin kaunar shan fitsarinta
- Carrie ta tsiri wannan dabi'a ce mai ban mamaki a matsayin zabi ga maganin ciwon dajin melanoma da aka gano tana dauke dashi
- Matar 'yar shekaru 53 da ba ta da niyyar daina wannan dabi'ar nan kusa ta ce fitsarin nata yana da dandano kamar kayan champagne a wasu lokutan
Coloado, Amurka - Carrie, mai shekaru 53 uwa ce wadda ta kirkiro wata dabi’a mai ban mamaki ta shan fitsarin da ta tsula kuma ta shafe shekaru hudu da suka gabata tana yin hakan.
Ba wai kawai tana shan fitsarin bane, tana amfani da shi a matsayin man goge hakora, tana shafa shi a karkashin idonta, sannan ta tsefe gashinta da dai sauran abubuwan kula da jiki na yau da kullum.
Carrie ta ce fitsarinta yana da dandano kamar abin sha na champagne
Da take magana a shirin TLC na My Strange Addiction, matar da ta fito daga garin Colorado a kasar Amurka ta ce yanayin fitsarin nata ya danganta da kalar abincin da ta ci a ranar.
Carrie ta ce wani lokaci yana da dandano mai gishiri-gishiri wani lokacin kuma kamar abin sha champagne.
Matar dai tana shan gilashi har guda biyar na fitsarinta a rana, wanda adadinsa ya kai akalla lita 3406 tun lokacin da ta kamu da jarabar shan fitsarin shekaru hudu da suka gabata.
A cewarsa:
"Wani lokaci yana da dandano mai gishiri-gishiri, wani lokacin yana dandano kamar shampagne."
Ta kuma bayyana cewa, a yanzu akwai abubuwa da dama da ta daina ci ko sha saboda rashin amintar dasu idan aka yi la'akari da sake amfani dasu; sabanin fitsari.
Yadda Carrie ta fara shan fitsari
Jaridar The Sun ta Burtaniya ta ruwaito cewa Carrie ta fara kwankwadar fitsarinta ne bayan da aka gano tana dauke da cutar daji mai suna melanoma shekaru hudu da suka gabata.
Maimakon mika kanta ga tsarin maganin ciwon daji da aka fi sani da 'chemotherapy', Carrie zabi magance ciwon ta hanyar shan fitsari wanda aka ce ya fi saukin kudi kuma tsohuwar al'ada ce da ake yi shekaru da dama.
Matar mai wani adadi na 'ya'ya duk da cewa ta bayyana rashin imani da maganin gargajiya ta kuma ki amince da za ta daina shan fitsari da sunan magani.
Carrie ta bayyana cewa:
"Daga duk abin da na karanta, idan na daina zan mutu."
Wata masaniyar abinci mai gina jiki mai suna Amanda Ursell ta shaidawa jaridar The Sun ta Burtaniya cewa, jama'a su fa sani, babu wasu sinadirai a cikin fitsari da ke da amfani a jikin dan adam.
Kalli bidiyon:
Dadi kamar kifi da kaza: Jama'a sun kadu ganin shahararriyar mawakiya na cin kyankyaso
A wani labarin, wata mata daga Dar es Salaam a kasar Tanzaniya, ta zama maudu'in tattaunawa a Intanet yayin da aka gano tana kiwon kyankyasai don samun abinci.
Saumu Hamisi, wata mawakiya mai suna Ummy Doll, ta ce mutane sun yi ta maganganu da yawa a lokacin da suka ji tana ajiye kwarin domin ta ci soye.
Ta shaida wa BBC cewa:
"Wasu sun ce ni mahaukaciya ce amma kyankyasai suna kawo min kudi don haka ban damu da ra'ayin mutane ba."
Asali: Legit.ng