Yanzu-yanzu: Jami'in tsaro daya ya mutu yayin da sojoji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja

Yanzu-yanzu: Jami'in tsaro daya ya mutu yayin da sojoji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja

  • Jami’an tsaron Najeriya na ci gaba da samun galaba a yakin da suke da ‘yan bindiga a yankin Arewa maso tsakiyar Najeriya
  • Musamman a jihar Neja, jami'an tsaro na yin kakkausar ragargaza kan 'yan bindigan da suka addabi al'ummar yankin
  • A ranar Asabar, 16 ga watan Afrilu, sojojin sun dakile wani mummunan harin da 'yan ta'adda suka kai a wasu al'umomin jihar

Jihar Neja - Wasu ‘yan ta’adda masu yawan gaske a kan babura da ke wucewa ta Kapana, cikin karamar hukumar Munya a ranar Asabar, 16 ga watan Afrilu sun kai hari a wani yanki a karamar hukumar Shiroro.

Wata sanarwa da kwamishinan kananan hukumomi, masarautu, da tsaro na cikin gida na jihar Neja, Emmanuel Umar, ya fitar ce ta bayyana hakan.

Barnar 'yan bindiga a jihar Neja
Yanzu-yanzu: Jami'in tsaro daya ya mutu yayin da sojoji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sanarwar ta bayyana cewa, jami'an tsaro na hadin gwiwa da ke wurin sun fatattaki 'yan bindigar, kamar yadda Legit.ng ta samo.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A cikin mummunan artabu, an kashe ‘yan ta’adda da dama, yayin da wasu suka samu raunuka, daya daga cikin jami’an tsaro, abin takaici, ya rasa ransa, wani kuma ya samu rauni.
“Gwamnatin jihar Neja za ta ci gaba da yin aiki tukuru wajen tallafa wa jami’an tsaronmu domin ganin an tafattaki wadannan miyagun da kuma kawar da su daga yankunanmu da a da ake zaman lafiya."

Hakazalika, sanarwar ta bayyana cewa, gwmanan ya ce zai ba da cikakken kayan aiki domin ganin an fatattaki 'yan bindiga.

A bangare guda, sanarwar ta bayyana rokon gwmanan ga jami'an tsaro kan su ci gaba da aikinsu yadda ya kamata domin wanzar da zaman lafiya da ragargazar 'yan ta'adda.

Wa'adin awa 24 ga dangin basaraken Abuja: Ko ku biya N6m ko kuma kunsan sauran, inji 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Gwamnatin Amurka ta amince Buhari ya kashe $1bn domin shigo da wasu jiragen yaki

A wani labarin, wadanda suka yi garkuwa da Hassan Shamidozhi, basaraken garin Bukpe da ke yankin Kwali na birnin tarayya Abuja, sun ba iyalansa wa’adin awa 24 su kawo naira miliyan 6 ko kuma su rasa shi.

Yan bindigar sun yi garkuwa da basaraken ne makonni biyu da suka gabata sannan suka nemi a biya kudin fansarsa naira miliyan 20.

An tattaro cewa sun rage kudin zuwa naira miliyan 6 bayan tattaunawa da aka yi da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.