Akan idon 'yan sanda 'yan daba suka kwashe mana dukiyoyi cikin sa'a 11, 'Yan kasuwa

Akan idon 'yan sanda 'yan daba suka kwashe mana dukiyoyi cikin sa'a 11, 'Yan kasuwa

  • 'Yan kasuwar Okobaba Sawmill dake cikin garin Legas suna cigaba da kirga irin asarar da suka tafka bayan 'yan ta'adda sun auka kasuwar misalin karfe 5:00 na yammacin Juma'a
  • An gano yadda hatsabiban suka ci karensu ba babbaka, inda suka balle shaguna 35 a kasuwar ba tare da jami'an tsaro sun iya wani abu a kai ba
  • 'Yan kasuwan sun koka game da yadda 'yan sanda suka aje motocinsu daga can nesa suna kallon barayin na loda kayan a motar tun karfe 5:00 na yamma har zuwa 4:00 na safe

Legas - 'Yan kasuwa da dama a Okobaba Sawmill dake cikin garin Legas na kirga yawan asarar da suka tafka bayan 'yan ta'adda sun auka kasuwar misalin karfe 5:00 na yammacin Juma'a, gami da dibar kayayyakin kusan shaguna 35.

Kara karanta wannan

An kaiwa jirgin kasan Abuja-Kaduna hari ne don koyawa El-Rufa'i darasi

Daily Trust ta gano yadda 'yan fashi da makamin suka ci karensu ba babbaka har kusan karfe 4:00 na safiyar Asabar, sannan suka taho da motar da zata kwashe kayan da suka sata.

Akan idon 'yan sanda 'yan daba suka kwashe mana dukiyoyi cikin sa'a 11, 'Yan kasuwa
Akan idon 'yan sanda 'yan daba suka kwashe mana dukiyoyi cikin sa'a 11, 'Yan kasuwa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An gano yadda 'yan sandan marabar Adekunle da Denton suka ji tsoron shiga Sawmill, wacce ke kauyen.

Kamar yadda bincike ya nuna, abunda ya jawo fashi da makamin ya fara ne a matsayin rikici tsakanin yara daga Jebba da layikan Ibadan da abokan hamayyarsu daga layin Abeokuta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyoyin da suka zanta da Daily Trust sun bayyana sunan wasu 'yan kungiyoyin 'yan ta'adda kamar haka; Omo B, Baba Muru, Gideon, Abu Inigho, Ila da Epon.

Babban Sakataran kungiyar Sawmillers na cikin garin Legas, Mr Titus Ikuejamoye, ya bayyanawa Daily Trust yadda barayin suka sace jannaretoci, kayayyakin waya, firiza da kayayyakin gini na miliyoyin naira.

Kara karanta wannan

Wa'adin awa 24 ga dangin basaraken Abuja: Ko ku biya N6m ko kuma kunsan sauran, inji 'yan bindiga

A cewarsa, "Misalin karfe 5:00 na yammacin Juma'a, yaran nan suka auka kasuwar sawmill da bindigoginsu. Kowa ya yi mamakin ganin yadda irin haka zai iya faruwa da rana tsaka. Suna ta harbi a iska. Nayi kokarin tserewa, gami da kiran DPO ofishin 'yan sandan Adekunle, inda na labarta masa abunda ke faruwa.
"Na kara da kiran wani 'dan sanda a marabar 'yan sandan Denton, ya ce min akwai tawagar dake tafe. Abun mamaki, ko da 'yan sandan suka iso, aje motocinsu suka yi daga nesa suna kallon yaran na kwashe mana kayayyakin shaguna.
"Suna ta dibar kayayyakin shagunan har zuwa misalin karfe 4:00 na safiyar Asabar. Har suna zuwa da motar don kwashe kayan da suka sace. Sun dauke jenaretoci, kayayyakin waya, firiza da kayayyakin gini. Nayi kokarin kiran 112 so uku, amma bata shiga ba."

Ikuejamoye ya ce babu wani rikici da ya hada 'yan kasuwan sawmill da hatsabiban, inda ya ce 'yan fashin sun nemi rikicin ne a matsayin dabarar da za suyi wa mutane fashi.

Kara karanta wannan

Jami’an tsaro sun yi nasarar dakile wani hari kan kauyen Kaduna, sun kashe dan bindiga 1

Ya kara da cewa, "Sun raunata wani jami'in tsaron da ya yi kokarin hana su balle shagunan. Sun balle shaguna 20 karkashin gada wurin sawmill, sannan suka haye sama suka balle shaguna 15 da ake saida kayyakin gini cikin sawmill. Kusan wata daya da ya wuce, sun kona wani bangare na sawmill."

Sai dai, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce ba gaskiya bane cewa da ake 'yan sanda sun zura wa hatsabiban idon yayin balle shagunan, inda ya kara da cewa 'yan kasuwan su gabatar da shaidu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel