Tsoron harin 'yan ta'adda: Bidiyon jirgin sama na raka jirgin kasa ya janyo cece-kuce

Tsoron harin 'yan ta'adda: Bidiyon jirgin sama na raka jirgin kasa ya janyo cece-kuce

  • 'Yan Najeriya sun yi martani bayan bayyanar bidiyon jirgi mai saukar ungulu yana biye da jirgin kasa don gujewa farmakin 'yan ta'adda
  • Jama'a da yawa sun zargi cewa ko dai baki aka yi wa Najeriya da ta dauka wannan matakin a maimakon shawo kan matsalar rashin tsaro
  • Matasa da yawa sun zargi gwamnatin da raka asara da guda sannan kuma idan 'yan ta'addan suka so hatta jirgin saman za su iya harbowa

Bidiyon jirgin sama yana raka jirgin kasa inda za shi ya bai wa 'yan Najeriya mamaki da kuma tsoron irin tabarbarewar da tsaron kasar nan ke yi.

'Yan Najeriya a kafar sada zumuntar zamani sun yi martani kan bidiyo jirgin sama yana raka jirgin kasa zuwa inda zai je. Wannan a bayyyane yake an yi shi ne domin bai wa jirgin kasan kariya gudun farmakin 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso Ya Bayyana Lokacin Da Zai Ƙaddamar Da Takararsa Na Shugabancin Ƙasa

Tsoron harin 'yan ta'adda: Bidiyon jirgin sama na raka jirgin kasa ya janyo cece-kuce
Tsoron harin 'yan ta'adda: Bidiyon jirgin sama na raka jirgin kasa ya janyo cece-kuce. Hoto daga @WEchefula
Asali: UGC

Ga martanin da 'yan Najeriya suka yi:

The Prince cewa yayi:

"Wannan rashin hankali ne. Me yasa muke asara a Najeriya ne? Jirgin sama na sintiri a titin jirgin kasa ko akan jirgin kasa. Waye ya tsinewa Najeriya? Nawa ne kudin kula da jirgin sama kuma nawa jirgin kasa ke kawowa? Ban gane ba gaskiya, me yasa?"

@BPK_007 ya ce:

"'Yan bindiga ne za su ga jirgin saman su tsere ko mene? Ban gane ba."

El-Amin Dahunsi ya ce:

"Wa ya tsine wa wani? Wannan matakin na yanzu ne fa har sai an ga bayan ta'addancin tare da dawo da kwarin guiwar matafiya. Kasuwancin sufurin jiragen kasa a halin yanzu ba kasuwanci bane, amfaninsa shi ne habaka ababen more rayuwa."

Popson ya ce:

Kara karanta wannan

Kawai ka bude gidajen yari kowa ya fito: Babban Lauya ga Buhari kan yafewa Nyame da Dariye

"Suna bukatar karin jirgin yaki saboda tsare jirgin saman saboda RPG za ta iya harbo wannan jirgin."

Codegidi.eth cewa yayi:

"Kuna bukatar motocin yaki domin bude layikan dogon. Me zai sa ba za mu raka kowanne jirgi da zugar sojoji ba?"

Romel Ugoji:

"Wannan daidai yake da amfani da garkuwa wurin magance harbin bindiga. Wannan zai kuwa bar karakainar jiragen da yawa? Shin wannan zai yi amfani? A'a, wannan ba mafita bace."

Abia First Son:

"Wannan ba zai bari ko tafiya daya cikakka ta kammalu ba. Wannan GPMG za ta iya harbo shi kuma a yi garkuwa da matukin jirgin."

Nomso:

"Kudin zuba wa jirgin sama mai babu shakka yana da yawa. Za a iya harbo jirgin saman idan an so saboda suna da makamai. Rance muke domin cin abinci yayin da gwamnati ta gaji, za su harbo su ne kawai a maimakon wannan shirmen. Farfagandar rashin hankali."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng