Sakin Dariye da Nyame: Bayan kwashe shekaru 11 a kotu, da kashe miliyoyin kudi, Shikenan: Lauyoyin EFCC

Sakin Dariye da Nyame: Bayan kwashe shekaru 11 a kotu, da kashe miliyoyin kudi, Shikenan: Lauyoyin EFCC

Hukumar hana almundahana da yiwa tatalin arzikin kasa zagon kasa ta kashe miliyoyin kudi wajen gurfanar da tsaffin gwamnonin Taraba da Plateau; Jolly Nyame da Joshua Dariye, Lauyoyi sun bayyana.

Jaridar Punch a tattaunawarta da wasu lauyoyi, masu bincike, da jami'an tsaron da suka tabbatar da ganin an hukunta gwamnonin biyu, sun ce Shugaba buhari ya watsa musu kasa a ido.

Jami'an EFCC da suka hukunta gwamnonin sun bayyana cewa ba karamin miliyoyi aka kashe tsakanin 2007 da 2018 ba.

Musamman, a cewarsu na Joshua Dariyae, wanda sai da aka rika kawo shaida daga Landan, Peter Clark, kuma ana biyan kudin kawoshi.

Nyame ya sace N1.16bn na jama'ar Taraba yayinda Dariye ya sace N2bn na jama'ar Plateau.

Kara karanta wannan

Ka yi abin kirki: Gwamnan PDP ya yabi Buhari kan yafewa Joshua Dariye da Jolly Nyame

Sai da aka fasawa wani dan sanda kai kan lamarin Dariye

Wani jami'in EFCC wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace sai mabiya Dariye fasa kan daya daga cikin yan sandan dake bincikensa Ilyasu Kwarbai, da gindin bindiga a Jos.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Yafewa Dariye ya karya mana karfin gwiwa. Mun kashe mafi yawan kudi wajen bincike. Daga Landan aka fara. Haka muke zuwa can kuma mu kwana a Otal."
"Peter Clark, wani jami'in dan sanda a Birtaniya ne babban shaida. Shi ya fara kama Dariye a 2004. Sai da muka kawo shi Najeriya lokuta da dama. Wasu lokutan sai ya dira Najeriya Alkali zai dage zaman dan wasu dalilai, haka zai koma kasarsa ya sake dawowa."
"Clark ne wanda ya bayyana yadda Dariya ya sayi biro £7,000 kuma aka kamashi da kudi sama da £40,000, yayinda aka kama hadimarsa na kimanin £50,000."

Kara karanta wannan

Kawai ka bude gidajen yari kowa ya fito: Babban Lauya ga Buhari kan yafewa Nyame da Dariye

"Mun kashe daruruwan miliyoyi kan wannan kes din. Har yanzu akwai alamun bugun da aka yiwa Kwarbai a kansa. Ta yaya Birtaniya za ta daukemu mutanen kirki?"

Sakin Dariye da Nyame
Sakin Dariye da Nyame: Bayan kwashe shekaru 11 a kotu, da kashe miliyoyin kudi, Allah ya isa: Lauyoyin EFCC
Asali: Twitter

Jawabin Lauyan da ya kwashe shekaru yana zuwa kotu

Hakazalika jaridar Punch tace Lauyan da EFCC ta dauka haya wajen gurfanar da tsaffin gwamnonin, Rotimi Jacobs, ya bayyana bacin ransa bisa abinda Buhari yayi.

Jacobs yace sakon da Buhari ya aikewa shine talaka kadai ya cancanci zama a gidan yari, kuma wannan zai karfafa matasa wajen dogewa kan sata da almundahana.

A cewarsa:

"Yafe musu na nuna cewa zasu iya neman a zabesu a wani mukami. Ikirarin yaki da rashawa ya zama wasa. Wannan koma baya ne sosai ga yaki da rashawa. Suna barin mumunan misali wa matasa."
"Mun dauko karar nan daga babbar kotu zuwa kotun koli amma yanzu an yafe musu."
"Wannan zai ragewa Alkali karfin gwiwa, da masu bincike, da lauyoyi."

Kara karanta wannan

Bidiyon cikin tamfatsetsen gidan Hassan Ayariga mai dakunan bacci 10, silma da wurin aski

Shahrarren marubuci, Farfesa Wole Soyinka, kuwa cewa yayi ya rasa abinda zai fadi.

"Babu abinda zan fadi illa shikenan. Shikenan kawai," yace.

Shugaban kungiyar Transparency International a Najeriya, Auwal Rafsanjani, ya ce gwamnatin Shugaba Buhari ta daina cewa mutane tana yaki da rashawa. Ya ce ko shakka babu wannan abu bai rasa alaka da zaben 2023.

Yace:

"Gwamnatin Buhari ta nuna cewa yaki da rashawarta dama yaudara ce, dama mulki take so don ta rufawa abokanta asiri. Ta rusa dukkan kokarin cewa EFCC da ICPC ke yi."
"Kar ka so ka san adadin kudaden da aka kashe wajen gurfanar da mutanen nan.... Ta wani dalili gwamnati zatayi asarar dukiyar al'umma idan ta san haka za tayi?"
"Ba mamaki saboda zaben 2023 ya gabato, kuma tsaffin gwamnonin biyu an yafe musu ne don jam'iyya mai mulki ta lashe zaben jihohin. Akwai dubunnan yan Najeriya dake kurkuku. Me yas aba za'a yafe musu ba? Me yasa wadanda suka halaka al'umma, suka takaita mutane ake yafewa?

Kara karanta wannan

Bala Mohammed: Buhari ya yi rugu-rugu da Najeriya amma ni zan gyara ta

Ortom, Jang sun jinjinawa Buhari

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, a ranar Juma’a, ya bayyana godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da majalisar kolin kasa bisa afuwar da suka yi wa Nyame da Dariye.

Qwamnan ya godewa shugaba Buhari da majalisa da kuma gwamnatin tarayya bisa wannan matakin duk da cewa ya yarda cewa lallai an koyi darassu masu amfani daga lamarin.

Tsohon Gwamnan jihar Plateau, Jonah Jang, ya bayyana cewa afuwar da shugaba Buhari ya yiwa tsohon gwamnan Plateau Joshua Dariye da tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame abin farin ciki ne.

Sanata Jang wanda ya bayyana farin cikinsa bisa wannan abu ya yi kira da tsaffin gwamnonin biyu idan sun fito su mayar da hankali wajen cigaban kasa.

Kawai ka bude gidajen yari kowa ya fito: Babban Lauya ga Buhari kan yafewa Nyame da Dariye

Shararren Lauya, Femi Falana, a ranar Juma'a, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya bude gidajen yari gaba daya a saki dukkan wadana aka daure kan laifin sata.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun halaka basarake da wasu mutum 24, sun sace babura a Benue

Falana ya bayyana hakan ne yayin jawabi a taron tunawa da marigayi Yinka Odumakin a jihar Legas, rahoton Vanguard.

Ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi adalci da daidaito tsakanin yan kasa saboda haka wajibi ne a saki dukkan wadanda tsare a kurkuku kan laifin sata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng