Bidiyon cikin tamfatsetsen gidan Hassan Ayariga mai dakunan bacci 10, silma da wurin aski

Bidiyon cikin tamfatsetsen gidan Hassan Ayariga mai dakunan bacci 10, silma da wurin aski

  • Dan siyasa kuma dan kasuwan Ghana, Hassan Ayariga ya mallaka wani tamfatsesen gida da motocin miliyoyin kudi
  • Katafaren gidan mai matukar birgewa ya kunshi dakunan kwana 10, dakin cinema da madafi har hudu
  • Gidan mai matukar izza yana da wurin shan iska biyu, shagon aski, wurin gyaran jiki da kuma hanyar da ta hada dakunan baccin

Ghana - Wanda ya kafa jam'iyyar All People's Congress (APC), Hassan Ayariga, ya na daga cikin mutane da suka fi kowa arziki a kasar Ghana duk da har yanzu jama'a basu san adadin dukiyar da ya mallaka ba.

Dan siyasan Ghanan ya mallaka katafarun gidaje masu izza a kasar. Gidan Ayariga da ya lakume miliyoyin daloli yana da dakunan bacci 10, dakin cinema da kuma katafarun madafi hudu.

Kara karanta wannan

Yaudara da neman goyon baya: Martanin Shehu Sani kan ikirarin Osinbajo na bin sahun Buhari

Bidiyon cikin tamfatsetsen gidan Hassan Ayariga mai dakunan bacci 10, silma da wurin aski
Bidiyon cikin tamfatsetsen gidan Hassan Ayariga mai dakunan bacci 10, silma da wurin aski. Hoto daga Kofi TV
Asali: UGC

Sauran kayan alatu

Katafaren gidan ya na da wuraren shan iska biyu, shagon aski, wurin gyara jiki da kuma wata hanya da ta hada dakunan baccin biyu.

Baya ga zamansa fitaccen dan siyasa kuma dan kasuwa, Hassan Ayariga sananne ne a fannin bayyana motocin alfarma.

Dan takarar shugabancin kasan na 2012 an saba ganinsa a gari cikin manyan motoci.

Kayataccen bidiyon cikin gidan Ayariga ya bayyana kuma ya kayatar. Kalle shi a kasa:

Gwarzon namiji: Matashin da yayi wuff da mata 9 a rana 1 yace yana son karin wasu 2

A wani labari na daban, wani matashi mai suna Arthur O Urso, wanda ya auri mata 9, ya bayyana cewa yana son ya auri wasu mata biyu don kai adadin matansa zuwa 10 tunda daya na son fita.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun halaka basarake da wasu mutum 24, sun sace babura a Benue

Mirror.co.uk ta ruwaito cewa, dan asalin kasar Brazil din ya zama abin burgewa a intanet a shekarar 2021 bayan ya bi kanun labarai bayan ya tare da mata 9 a lokaci daya a wani karamin biki da ya gudana a birnin São Paulo na kasar Brazil.

Mahaifin yaro dayan da farko yana tare da matarsa ta farko mai suna Luana Kazaki amma daga bisani suka kulla aure da ita yayin da ya auri sauran 8 a lokaci daya.

Sai dai kuma, daya daga cikin matan mai suna Agatha ta rabu da shi kuma tana bukatar saki saboda tace tana kewar zamanta mace daya a wurin mijinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel