Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

  • ‘Yan bindiga sun shiga cikin al’ummar jihar Filato akan babura sama da 70, sun yi harbe-harbe da kone-kone
  • Rahotanni sun ce kawo yanzu an binne gawarwaki 106 yayin da al’ummomin da abin ya shafa ke ci gaba da zakulo gawarwakin wadanda harin ya rutsa dasu
  • Wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su a halin yanzu suna samun kulawa a asibiti yayin da wasu daruruwa suka koma gidajensu

Kanam, Filato - Akalla mutane 106 ne ya zuwa yanzu aka ce an binne sakamakon hare-haren da aka kai kan al’umomin jihar Filato a kwanakin nan.

Shugaban karamar hukumar Kanam ta jihar Filato Dayabu Garga ne ya bayyana hakan, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Amurka ta amince Buhari ya kashe $1bn domin shigo da wasu jiragen yaki

Barnar 'yan bindiga a jihar Filato
An binne mutane samda da 100 ya zuwa yanzu | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Da yake karin haske game da sake barkewar rikici a wasu sassan jihar ta Arewa ta Tsakiya, Garga ya ce:

"Ina nan a ranar Litinin da safe lokacin muka yi jana'izar mutane 106 da aka kashe kuma muna ci gaba da diban gawarwaki a nomaki."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar shugaban, sama da mutane 16 ne ke kwance a asibiti sannan daruruwan mutane sun rasa matsuguninsu, wanda hakan ke kara yawan ‘yan gudun hijira a yankin.

Wasu ‘yan ta’adda da yawansu ya kai 70 a kan babura ne suka kai hari a kauyuka 10 da ke karamar hukumar a ranar Lahadi, 10 ga watan Afrilu, inda suka kashe mazauna garin ba gaira ba dalili.

Kauyuka 10 da aka kai harin a Garga sun hada da Kukawa, Gyanbawu, Dungur, Kyaram, Yelwa, Dadda, Wanka, Shuwaka, Gwammadaji, da Dadin Kowa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta fara rabon buhunan abinci kamar yadda Buhari ya bada umarni

Jama'a na bukatar karin tsaro

Da yake kokawa kan hare-haren na baya-bayan nan, Garga ya yi kira da a kara ba da kariya ga mutanensa.

Shugaban karamar hukumar ya shaida wa Nigerian Tribune cewa jami’an karamar hukumar tare da mafarauta da ’yan banga suna ci gaba da toshe hanyoyi da ke kewaye tare da hada gwiwa wajen kwaso gawarwakin wadanda suka bace.

Garga ya bayyana cewa an tura karin jami’an tsaro tare da kwace garuruwa da kauyukan da lamarin ya shafa.

Ya kara da cewa wadanda ‘yan ta’addan ba su kone gidajensu ba sun dawo yayin da wadanda ba su aka kone nasu a halin yanzu ke fakewa a unguwar Garga.

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka hallaka wani, suka sace 'yarsa mai shekaru 15 a Zaria

A wani labarin, wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Dorayi da ke unguwar Dutsen Abba a karamar hukumar Zaria, inda suka kashe wani Alhaji Abdullahi Ardo tare da sace ‘yarsa mai shekaru 15 mai suna Mariya.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda hudu har lahira

Wani ganau ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 2 na safe, inda suka tafi kai tsaye gidan marigayin, inji rahoton Daily Trust.

Wani ganau ya ce:

“Daga nan ne suka tafi ba tare da kai hari a kan wani gida ko mutum ba. Muna jin sun zo ne musamman don daukar Alhaji Ardo, da suka yi yunkurin haka, watakila ya yi turjiya, shi ya sa suka harbe shi, sannan suka yi awon gaba da ‘yarsa.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.