Kada ku cire rai: Buhari ya jaddawa 'yan Najeriya cewa matsalar tsaro za ta kau nan kusa

Kada ku cire rai: Buhari ya jaddawa 'yan Najeriya cewa matsalar tsaro za ta kau nan kusa

  • Shugaban kasar Najeriya Manjo Muhammadu Buhari mai ritaya ya taya kiristoci murnar bikin Easter na bana
  • A cewar Buhari, sakon na Easter yana tunatar da ‘yan Najeriya karfin kauna, imani, da fansar Ubangiji a matsayin kasa daya
  • Shugaban a cikin sanarwar ya yi kira ga ‘yan kasar da su ci gaba da nuna soyayya ga juna, maimakon kyama tsakanin juna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su karaya wajen fuskantar kalubalen rayuwa.

Wannan na kunshe ne a cikin sakon da shugaban kasar ya aikewa ‘yan Najeriya gabanin bikin Easter na 2022 a ranar Alhamis, 14 ga Afrilu, ta hannun mai magana da yawunsa, Femi Adesina kuma ta shafin Facebook.

Alkawarin Buhari ga 'yan Najeriya
Kada ku cire rai: Buhari ya jaddawa 'yan Najeriya cewa zai magance matsalar tsaro | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shugaban wanda ya taya mabiya addinin Kirista murna ya ce bikin na bana ya sha bamban sosai ga mabiya addinai biyu a Najeriya domin kuwa an kammala kwanaki 40 na Azumin Kiristoci da rabin Azumin watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Matsaloli ta ko ina: Najeriya na bukatar shugabanni masu tsoron Allah, inji malamin addini

A cewarsa, Easter na kuma kara kaimi da juriyar ruhin dan Adam na rashin cire rai da fuskantar kalubale na rayuwa.

Buhari ya bayyana fatansa na cewa halin da ake ciki na rashin tabbas da rashin tsaro nan ba da dadewa ba za su kau nan kusa.

Shugaban Najeriya ya kuma roki 'yan kasa da su wanzar da kaunar juna maimakon kiyayya

Yace:

“Wannan lokacin yana karfafa mana imani cewa halin da ake ciki na rashin tabbas da rashin tsaro nan ba da jimawa ba zai kai a samu nasara akan muggan ayyuka; fata a kan yanke kauna, haske kan duhu.
"Ina rokon mu da mu kara kaunar juna maimakon kiyayya, mu kara nuna kishin kasa, kasancewar kasar nan ce kadai muke da ita."

Kara karanta wannan

Ko Buhari ya sauka matsalar tsaro ba za ta kare ba, Fadar Buhari ga dattawan Arewa

Yayin da ake ta cece-kuce kan man fetur, majalisa ta amince da bukatar Buhari na kashe N4tr a tallafin mai

A wani labarain, majalisun dokokin kasar nan sun amince da bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bijiro da ita na ware naira tiriliyan 4 na kudin tallafin man fetur, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

Majalisar dattawa da ta 'yan majalisu sun amince da bukatar shugaban kasar ne bayan sun yi la’akari da rahotannin kwamitocinsu kan harkokin kudi.

Amincewar ta biyo bayan bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi na sake fasalin kasafin kudin shekarar 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel