'Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sako Ɗalibai Mata Na Kwallejin Lafiya Ta Zamfara
- Dalibai mata hudu na Kwallejin Kimiyya da Fasahar Lafiya ta Tsafe da ke Jihar Zamfara sun kubuta daga hannun yan bindiga
- Kakakin yan sandan Jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ya tabbatar da lamarin ya kuma ce an sada su da yan uwansu bayan duba su
- Shehu ya ce ba shi da masaniya kan maganar biyan fansa kafin a sako daliban na Kwallejin ta Tsafe
Tsafe, Zamfara - An sako dalibai hudu na Kwallejin Kimiyya da Fasahar Lafiya ta Tsafe da ke Jihar Zamfara.
Yan bindigan sun sace dalibai mata biyar ne a yayin da suka kutsa dakin kwanan daliban da ke wajen makaranta a ranar Laraba.
Daya daga cikin wadanda aka sace ta tsere a yayin da ake kokarin tafiya da su.
Rundunar yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da sakin daliban hudu
Da ya ke tabbatarwa The Cable, Kakakin yan sandan Jihar Zamfara, Mohammed Shehu, a ranar Juma'a ya ce daliban hudu da aka sace sun dawo.
Kakakin yan sandan bai yi tsokaci kan cewa ko an biya fansa ba kafin sako su.
A sakon text da Shehu ya aike wa The Cable, ya ce:
"Da gaske ne, dalibai hudun da aka sace sun samu yanci, an musu gwajin lafiya, yan sanda sun musu tambayoyi sannan an sada su da yan uwansu.
"Ba mu da masaniya kan maganar biyan kudin fansa."
Rahoton da TVC News ta wallafa ya ce yan bindigan ne kawai suka sako su domin ra'ayin kansu.
Masu garkuwar ne don kashin kansu suka sako daliban a garin Hegin Baza, a karamar hukumar Tsafe a cewar rahoton.
'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed
A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.
Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.
Asali: Legit.ng