Yadda kanin mijina ya babbaka mijina, Mai juna biyu ta bada labari mai ban tausayi a bidiyo

Yadda kanin mijina ya babbaka mijina, Mai juna biyu ta bada labari mai ban tausayi a bidiyo

  • Wata 'yar Najeriya wacce 'dan uwan mijinta ya babbaka mijinta, Ifeanyi Njokure, da ransa ta koka game da rashin da tayi mai cike da ban tausayi a wani bidiyo dake tashe
  • Matar mai suna Princess Munachi ta bada labarin abunda ya faru a ranar, yayin da Benjamin Ogudoro, wanda aka zarga da halaka mijinta ya kai masa harin
  • A cewar Munashi, mutumin ya shigo yayin da mijinta da 'yar uwar mijinta ke bacci, inda ya antaya musu fetur gami da banka musu wuta suka kone

Legas - Princess Munachi, mata mai dauke da juna biyu, wacce 'dan uwan mijinta mai suna Benjamin Ogudoro ya babbaka mijinta da ransa ta bayyana a wani bidiyo tana kuka cike da ban tausayi.

A cewar matar, wani Benjamin wanda a halin yanzu yake tsare a sashin binciken masu laifi na Legas ne ya halaka marigayin mijinta mai suna Ifeanyi Njokure.

Kara karanta wannan

Bana yi kuma: Budurwa ta soke aurenta ana saura kwana 3 saboda sun samu sabani da angon nata

Me zan sanar da yarana? Mai cikin da siriki ya halaka mijinta ta koka a bidiyo
Me zan sanar da yarana? Mai cikin da siriki ya halaka mijinta ta koka a bidiyo. Hoto daga @bbcnewspidgin
Asali: Instagram

Princess Munachi ta ce, a halin yanzu tana cikin rudanin abunda zai faru da 'ya'yanta.

Benjamin shine mijin Majela Chinyere Ogudoro, 'yar uwar marigayin, wanda ya dawo Najeriya daga Scotland a wannan bakar ranar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda lamarin ya auku

Yayin bada labarin mai girgiza zukata, Princess ta ce marigayin mijinta na bacci tare da 'yar uwarsa wacce itama ta rasa ranta a lokacin sanadiyyar babbakewar da tayi.

Ta ce, Benjamin da mijinta sun samu sabani. Benjamin ya dan fita bai sake dawowa ba sai da ya bari biyun suna bacci. Ya dawo da fetur, wanda ya antaya musu, tare da banka musu wuta.

Kalmominta: " Ta ya zan fadawa 'ya'yana mahaifinsu ya mutu? Ba hatsari ya yi ya mutu ba, ba ciwo ya yi ba. Ta ya zan fara fada musu babbakashi akai?

Kara karanta wannan

Ramadan: Magidanci ya lakada wa matarsa mai ciki mugun duka kan abincin Sahur

@bbcnewspidgin ne suka wallafa bidiyon a shafinsu na Instagram.

Bidiyon dankareriyar budurwa tana watsi da abinci da zoben da saurayi ya bata na neman aurenta

A wani labari na daban, Wani matashi 'dan Najeriya ya kwashi kashinsa a hannu yayin da yayi kokarin neman auren budurwarsa , inda ta ki yarda da bukartarsa ta hanyar cin zarafinsa.

@ourtalkroom ne suka wallafa yadda lamarin, ya auku a wani gidan saida abincin da ba a bayyana ba, wanda ya tada kura a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.

A bidiyon anga yadda mutumin ya sanya guiwarsa a kasa rike da zobe yayin da ya roki kuttubar budurwarsa ta amince ta aureshi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel