Sabon hari: An sheke dan bindiga yayin da gungunsu suka kai hari ofishin 'yan sanda

Sabon hari: An sheke dan bindiga yayin da gungunsu suka kai hari ofishin 'yan sanda

  • Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta dakile harin 'yan bindiga a jihar, an hallaka wani dan bindiga
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da 'yan bindiga ke ci gaba da kai munanan hare-hare yankunan jihar ta Anambra
  • Rahoto ya bayyana cewa, yanzu haka an kwato makamai da layu daga hannun 'yan bindigan da suka tsere

Anambra - Jaridar Punch ta ruwaito cewa, rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, da sanyin safiyar ranar Alhamis, ta dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a hedikwatar hukumarta ta Nteje, a karamar hukumar Oyi ta jihar.

Hakan dai ya biyo bayan kiran da aka yi na kawo dauki ne a yayin da wasu gungun ‘yan bindiga suka kai wa ofishin hari.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda hudu har lahira

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Echeng Echeng ne ya jagoranci aikin dakile harin da misalin karfe 3 na safe.

'Yan bindiga sun kai hari Anambra, an kashe daya daga cikinsu
Sabon hari: An sheke dan bindiga yayin da gungunsu suka kai hari ofishin 'yan sanda | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An kashe daya daga cikin ‘yan bindigar yayin da sauran ‘yan kungiyar suka tsere daga wurin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kayayyakin da ‘yan sandan suka kwato sun hada da bindiga kirar O6 guda daya, mujalla daya da alburusai 53 masu girman 5.56mm da kuma layu.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce:

“Jami’an ‘yan sandan sun fatattaki maharan.
“A yayin fafatawar da aka yi da bindigar, an kashe daya daga cikinsu, kuma saboda yadda jami’an ‘yan sandan suka fatattakesu, sauran maharan sun gudu daga wurin. An tsare ofishin kuma duk jami’an ‘yan sanda da makamai suna nan lafiya."

Kwamishinan, ya nanata cewa rundunar ba za ta bari wasu bata gari su dakushe zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma ba.

Kara karanta wannan

Jami’an tsaro sun yi nasarar dakile wani hari kan kauyen Kaduna, sun kashe dan bindiga 1

Tushen hare-hare a kudu maso gabas

Jami’an ‘yan sanda da cibiyoyin gwamnati na fuskantar munanan hare-hare musamman a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Gwamnatin Najeriya takan zargi haramtacciyar kungiyar 'yan aware ta IPOB da kai hare-haren. Sai dai kungiyar ta sha musanta hannu a hare-haren.

Kungiyar IPOB ce ke jagorantar fafutukar neman kafa kasar Biafra mai cin gashin kanta daga yankin Kudu maso Gabas da kuma wasu yankunan Kudu maso Kudu.

Shugaban kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu, yanzu haka yana tsare a Abuja inda yake fuskantar shari’a bisa zarginsa da cin amanar kasa.

Za mu bayyana sunayen wadanda suka kai harin jirgin kasan Abuja-Kaduna, FG

A wani labarin, Gwamnatin tarayya a jiya ta sanar da cewa nan babu dadewa za ta bayyana sunayen wadanda suka kai farmakin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Gwamnatin ta dora laifin mummunan lamarin da ya faru kan abinda ta kwatanta da gamayyar Boko Haram da 'yan binidga da ke cin karensu a yankin, ThisDay ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun halaka basarake da wasu mutum 24, sun sace babura a Benue

Gwamnatin tarayyar ta ce duk da jami'an tsaro na aiki kan bankado kungiyar da ta kai mugun farmakin, binciken farko ya nuna cewa farmakin gamayya ne tsakanin kungiyoyin ta'addanci, inda aka yi kira ga 'yan Najeriya da su hada kai da gwamnati domin bankado su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.