Bayan zargin kin jinin Musulunci, Osinbajo ya saki bidiyon Musulman dake aiki karkashinsa

Bayan zargin kin jinin Musulunci, Osinbajo ya saki bidiyon Musulman dake aiki karkashinsa

  • Ofishin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ta yi watsi da zargin cewa bai son Musulmai
  • Kungiyar MURIC da Farooq Kperogi, wani Malamin jarida a Amurka sun zargi Osinbajo da kin jinin addini
  • Saboda haka, Osinbajo ya saki bidiyon jerin ma'aikatan dake aiki karkashinsa a fadar shugaban kasa

FCT Abuja - Sakamakon zarge-zargen da ake yiwa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, na nuna bangarancin addini da kin jinin Musulmai, ya saki sabon bidiyo.

TheCable da PremiumTimes sun sami bidiyon daga ofishin mataimakin shugaban kasa ranar Laraba, 13 ga watan Afrilu, 2022 wanda ke nuna ma'aikata Musulmai dake aiki da Osinbajo.

A bidiyon, mutum 16 sun bayyana cewa su Musulmai ne kuma sunyi aiki da mataimakin shugaban kasan.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin sunayen masu takarar shugaban kasa na APC da PDP

Wasu na cigaba da aiki da shi kuma an sallami wasu cikinsu.

Osinbajo
Bayan zargin kin jinin Musulunci, Osinbajo ya saki bidiyon Musulman dake aiki karkashinsa Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Ga jerin sunayensu:

1. Abdulrahman Ipaye (Lagos)

2. Mariam Uwais (Kano)

3. Babafemi Ojudu (Ekiti)

4. Balkisu Saidu (Sokoto)

5. Abdullahi Gwari (Yobe)

6. Olabisi Ogungbemi (Kwara)

7. Ahmad Zakari (Jigawa)

8. Afeez Kau (Kano)

9. Abdulrahman Baffa-Yola

10. Muhammed Braima (Kwara)

11. Yusuf Ali (Kwara)

12. Gambo Manzo (Gombe)

13. Mariam Masha (Lagos)

14. Muritala Aliyu (Kogi)

15. Ibrahim Salama (Katsina)

16. Lanre Sasere (Lagos)

Kalli bidiyon a nan :

Jawabin daya daga cikinsu

Legit a ruwaito Dr. Balkisu Saidu, babbar mai baiwa ofishin mataimakin shugaban kasan kan lamuran dokoki da bahasi da bayanin yadda Osinbajo ke mu'amalantarsu.

A cewar Saidu, saboda tsabar adalcin mataimakin shugaban kasar, ba a yin taro a ofishinsa a Aso Villa a duk lokacin da ya san musulmai su na zuwa yin sallah.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Buhari ya kira zaman dukkan masu mulki da tsaffin shugabannin Najeriya

Kamar yadda ta bayyana a rubutunta domin yin raddi, hadimar ta ce Osinbajo yana ware kudi daga alihunsa duk watan azumi domin yi wa musulmai buda-baki.

Farfesa Osinbajo bai jin wani abu saboda ya ga Balkisu Saidu sanye da zumbulelen hijabi, kamar yadda bai da matsala don an yi wata shiga ta dabam a ofishinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel