Yanzu-yanzu: Buhari ya kira zaman dukkan masu mulki da tsaffin shugabannin Najeriya

Yanzu-yanzu: Buhari ya kira zaman dukkan masu mulki da tsaffin shugabannin Najeriya

  • Shugaban Buhari na jagoratar majalisar koli ta kasa yau Alhamis a fadar shugaban kasa dake Abuja
  • Majalisar kolin ta hada da dukkan gwamnonin Najeriya, da tsaffin shugabannin kasar Najeriya
  • Wannan shine karo na hudu da Shugaba Buhari zai kira wannan zama tun da ya hau mulki a 2015

Aso Villa, Abuja - Yayinda Najeriya ke fama da matsaloli daban-daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya kira taron masu ruwa da tsaki da tsaffin shugabannin Najeriya.

Yanzu hakan shugaba Buhari na jagorantar zaman a fadar shugaban kasa, Aso Villa.

Wannan shine karo na hudu da Buhari zai kira wannan zama tun da ya hau mulki.

Na karshe da aka yi shine na Agustan 2020 yayinda cutar Korona tayi sauki.

An fara wannan zama misalin karfe 10 na safe.

Wadanda ke hallare sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha; NSA Babagana Munguno da Farfesa Ibrahim Gambari.

Kara karanta wannan

Bayan satar dukiyar al’umma, Buhari ya yafewa Joshua Dariye, Jolly Nyame, da wasu fursunoni 157

Buhari ya kira zaman dukkan masu mulki da tsaffin shugabannin Najeriya
Yanzu-yanzu: Buhari ya kira zaman dukkan masu mulki da tsaffin shugabannin Najeriya Hoto: @NigeriaGov
Asali: Twitter

Tsaffin Shugaban kasan dake hallare a wajen sun hada Abdusalami Abubakar; Yakubu Gowon da Goodluck Jonathan.

Sauran na hallara ta yanar gizo.

Gwamnoni dake hallare da kafafunsu sun hada da Kayode Fayemi (Ekiti); Hope Uzodinma (Imo) ; Atiku Bagudu (Kebbi); Bello Matawalle (Zamfara); Nasir El-rufa’i (Kaduna); Abdullahi Ganduje (Kano) da Abubakar Badaru (Jigawa).

Sauran gwamnonin na hallare ta yanar gizo.

Gabanin fara zaman, an yi addu'a ga tsohon shugaban kasan rikon kwarya, Ernest Shonekan, wanda ya mutu ranar 11 ga Junairu, 2022.

Abinda suka yanke

Majalisar magabatan ƙasar nan ta amince da gudanar da ƙidaya ta ƙasa a watan Afrilu, 2023 bayan kammala babban zaɓe, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Darakta Janar na hukumar kidaya ta ƙasa NPC, Nasir Isa-Kwarra, shi ya bayyana haka ga manema labaran gidan gwamnati bayan taron majalisar bisa jagorancin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Isa-Kwarra ya ƙara da cewa hukumar NPC zata gudanar da gwajin kidaya a watan Yuni, 2022 bayan jam'iyyun siyasa sun kammala harkokin su na zaɓen fidda gwani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel