Yadda Jami’an tsaro ke taimakawa ‘Yan ta’adda – Majalisar Tarayya ta yi babban fallasa

Yadda Jami’an tsaro ke taimakawa ‘Yan ta’adda – Majalisar Tarayya ta yi babban fallasa

  • ‘Yan majalisar wakilan tarayya sun yi Allah-wadai da matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a kasa
  • A ‘yan kwanakin nan ‘yan bindiga sun kashe rayuka bila-adadin musamman a wasu jihohin Arewa
  • Hakan ta sa irinsu Hon. Usman Kumo suka bada shawarar a canza NSA da kuma Ministan tsaro

Abuja - Gidan talabijin na Channels TV ya rahoto cewa majalisar tarayya ta yi tir da kashe-kashen da aka yi kwanan nan a Benuwai, Taraba da jihar Filato.

Abin har ya kai wasu daga cikin ‘yan majalisar kasar sun bada shawarar a tunbuke Ministan tsaro da Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro.

Shugaban kwamitin harkokin ‘yan sanda a majalisar wakilai, Hon. Usman Kumo ne ya kawo shawarar a tsige Bashir Magashi da Babagana Monguno.

Kara karanta wannan

Ashe makiyaya ne ba ‘Yan bindiga ba – ‘Yan Sanda sun yi karin haske kan bidiyon da ke yawo

“Idan shugaban kasa ya na neman kasar nan da alheri, idan kuma ana neman mafita, dole ya yi gaggawar sauke NSA, sai kuma Ministansa na tsaro.”

- Hon. Usman Kumo

Kamar yadda Punch ta kawo rahoto a yammacin Laraba, ‘yan majalisar su na ganin jami’an tsaro su na taimakawa ‘yan bindiga da sauran masu addabar al’umma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bugu da kari, ‘yan majalisar sun ce kwalliya ba ta biya kudin sabulu a kudin da gwamnatin tarayya ta ke kashewa domin ta shawo kan matsalar tsaron ba.

Majalisar Tarayya ta yi babban fallasa
'Yan majalisar wakilan tarayya a wani zama Hoto: @HouseNGR / Facebook
Asali: Facebook

Zargin da ‘yan majalisar suke yi shi ne hafsoshin tsaro na amfana da matsalar da ake fama da ita, saboda irin kudin da ake warewa domin a zauna lafiya.

Wase ya zargi hukuma da laifi

Hon. Ahmed Wase wanda ya jagoranci zaman na jiya ya ce an samu wani soja da ya kamata a ce ya na Zamfara, da laifin rabawa ‘yan bindiga kayan sojoji.

Kara karanta wannan

Sabon hari: An kashe sabon sarkin gargajiya a yankin Kaduna, da wasu mutum 14

Mataimakin shugaban majalisar ya ce an gagara daukar mataki. Wase ya ce an kona gidaje 32 a kauyensa, mutane duk sun tsere domin su iya tsira a ransu.

Hon. Yusuf Gagdi ya yi magana kan harin da aka kai wa mutanen Filato. Bem Mzondu da John Dyegh sun kawo batun kashe-kashen da aka yi a Benuwai.

"Ina Shugaban kasa?"

Ba tare da jin nauyi ba, Hon. Gagdi ya ce babban nauyin da ke kan shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar nan.

An rahoto Hon. Fatuhu Mohammed ya na jefa irin wannan zargi ga hafsoshi, ya kuma ce akwai bukatar a ga laifin shugaban kasa da yadda ake kasafin kufi.

Abin da ya faru a Kaduna

Kwanan nan aka ji Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kaduna ya bayyana cewa ashe mutanen da aka gani an yi ram da su a wani bidiyo, ba ‘yan ta’adda ba ne.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Yi Amfani Da Malaman Addini Don Tuntuɓar 'Yan Bindiga, Farfesa Yusuf

Bincike ya nuna ‘yan bindiga ne suka kai hari a wani kauye, suka yi ta’adi, a karshe suka hada rigima tsakanin makiyaya Fulani da Gbagyi da ke garin Chikun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng