Gwamnati Ta Yi Amfani Da Malaman Addini Don Tuntuɓar 'Yan Bindiga, Farfesa Yusuf
- Farfesa Usman Yusuf ya yi kira ga gwamnatin tarayya akan ta tattauna da ‘yan bindiga ta hanyar amfani da shugabannin addini don shawo kan matsalar tsaro
- Ya yi kiran ne bayan ganin halin da kasa ta ke ciki wanda yanzu haka ake zargin ‘yan bindiga sun hada kai da mayakan ISWAP da Boko Haram
- Ya yi wannan kiran ne ta wata takarda wacce ya saki mai taken “mummunan hadin kan da ke tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan ISWAP matsala ce ga tsaron kasa”
Kaduna - An yi kira ga Gwamnatin Tarayya akan neman hanyar tattaunawa da ‘yan bindiga ta hanyar amfani da shugabannin addini a matsayin wata hanyar shawo kan hadin kan da ‘yan bindiga suka yi da mayakan ISWAP, Nigerian Tribune ta ruwaito.
Farfesa Usman Yusuf ne ya yi wannan kiran ta wata takarda wacce ya saki mai taken, “Mummunan hadin kan da ke tsakanin ‘yan bindiga da mayakan ISWAP barazana ce ga tsaron kasa” wacce ya ba manema labarai a Kaduna ranar Alhamis.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yusuf wanda farfesa ne a fannin lafiyar jini da dashen bargo, ya ce “an tashi da safiyar Litinin, 28 ga watan Maris din 2022 da mummunan labarin harin da ‘yan bindiga suka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna inda aka samu rashe-rashen rayuka da garkuwa da mutane da dama wadanda wasunsu ya san su.
Ya fara da mika ta’aziyya sannan ya shawarci gwamnati
Kamar yadda ya bayyana cikin takardar wacce Newstral ta bayyana:
“Muna mika ta’aziyya da addu’ar mu ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, sannan muna yi wa wadanda suka samu raunuka fatan samun lafiya yayin da yanzu haka ba a san inda wasu suke ba. Ina kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da ta zage wurin tabbatar da kowa ya dawo gida ga iyalansa lafiya.”
Ya ce bayan samun labarin harin da kuma yadda aka gudanar da shi, yana zargin aikin ‘yan ISWAP ne, ba aikin ‘yan bindigan da suka gani a ziyarar da suka kai dazukan jihohi 8 na arewacin Najeriya tare da Sheikh Dr Ahmed Gumi ba.
Kamar yadda ya shaida, a shekaru biyun da suka gabata, Sheikh Gumi ya ce masa ya kamata a je a samu ‘yan bindiga a yi musu wa’azi don su tuba kuma su zubar da makamansu kafin su hada kai da ‘yan Boko Haram da ISWAP.
Ya ce ‘yan Najeriya ba su san hadarin ISWAP ba
Kamar yadda ya ce:
“Abubakar Shekau, shugaban Boko Haram wanda ya mutu ya saki bidiyo yana sukar ziyarar da Sheikh Gumi ke kaiwa daji, saboda ya san hakan zai iya kawo cikas garesu yayin da suke kokarin hada kai da ‘yan bindigan.
“Duk wani hadin kan da ya auku tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan ISWAP zai kara rura wutar ta’addanci wanda hakan zai kara lalata harkar tsaron kasa.”
A cewarsa, ISWAP tana da tarihin lalata wuri da ta’addanci kamar yadda ta yi a Jihar Borno, kuma kila mutane da dama ba su san illarta ba saboda ba sa samun labaran yadda komai ya wakana.
Ya ce Maiduguri, babban birnin Jihar Borno tana cikin duhu babu wuta tun watan Janairun 2021, tsawon watanni 14, saboda ‘yan Boko Haram da ISWAP sun lalata hanyar wutar cikin garin har sau biyu.
'Yan Ta'adda Sun Afka Wa Mutane a Masallaci Yayin Buɗe-Baki, Sun Kashe 3 Sun Sace Wasu Da Dama
A wani labarin, A ranar Talata ‘yan bindiga sun kai farmaki masallaci inda suka afka wa wa mutane yayin da suke tsaka da yin buda-baki, wanda ya ja suka halaka mutane uku, Daily Trust ta ruwaito.
Daily Trust ta gano yadda ‘yan ta’addan suka isa da yawansu, har suka sace wasu da yawa a masallacin sannan suka zarce da su inda ba a sani ba.
An tattaro bayanai akan yadda lamarin ya auku a kauyen Baba Juli da ke karamar hukumar Bali a cikin Jihar Taraba.
Asali: Legit.ng