Ko Buhari ya sauka matsalar tsaro ba za ta kare ba, Fadar Buhari ga dattawan Arewa
- Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa, a halin yanzu dai ba saukar Buhari daga mulki bane mafita ga matsalar tsaro
- Wannan batu na zuwa ne a matsayin martani ga kalaman da dattawan Arewa suka tura na cewa, ya kamata Buhari ya sauka
- Dattawan Arewa sun nemi Buhari ya sauka daga kujerarsa ganin yadda ya gagara tabuka komai kan matsalar tsaro
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi watsi da kiran da dattawan Arewa suka yi na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi murabus sakamakon kalubalen tsaro da ake fuskanta a Arewa.
Kungiyar dattawan Arewa ta yi wannan kiran ne da yammacin ranar Talata 12 ga watan Afrilu, kamar yadda rahotanni suka kawo, Daily Trust ta ruwaito.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce murabus din shugaban kasar ba zai taba zama mafita ga matsalolin tsaron kasar nan ba.
Kakakin shugaban kasar, ya ce nan ba da jimawa ba za a fara gudanar da sauye-sauye a harkokin tsaron cikin gida.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kuma bayyana cewa tuni hukumomin tsaro suka kara kaimi wajen magance yawaitar ayyukan ta’addanci a baya-bayan nan, musamman a jihohin Kaduna da Neja da kuma yankin Neja Delta daidai da umarnin shugaban kasa.
A cewarsa, rundunar tsaron ta sake daidaituwa tare da sake tsara ayyukan da ake gudanarwa a yankunan da abin ya shafa domin samun sakamako mai kyau.
Fadar shugaban kasar ta zargi "masu zagon kasa" da nufin bata gwamnati da nuna ba za ta iya magance abubuwan da ke faruwa a kasar ba, kamar yadda Daily Post ta tattaro.
Dattawan Arewa sun bukaci murabus din Buhari, sun sanar da dalilinsu
A wani labarin, Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta bukaci murabus din shugaban kasa Muhammadu Buhari nan take sakamakon yawaitar kashe-kashe a fadin kasar nan ballantana arewaci.
Rashin Tsaro: Ra'ayin Shehu Sani Ya Banbanta Da Na Dattawan Arewa, Ya Ce A Ƙyalle Buhari Ya Kammala Wa'adinsa
Daily Trust ta ruwaito cewa, daraktan yada labaran kungiyar, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya yi wannan kiran a ranar Talata.
"Mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari bai magance kalubalen tsaro da muke ciki ba. Ba za mu cigaba da rayuwa tare da mutuwa a karkashin makasa, masu garkuwa da mutane, masu fyade da sauran kungiyoyin ta'addanci da suke hana mu hakkinmu na zaman lafiya da tsaro ba.
Asali: Legit.ng