Yaudara da neman goyon baya: Martanin Shehu Sani kan ikirarin Osinbajo na bin sahun Buhari

Yaudara da neman goyon baya: Martanin Shehu Sani kan ikirarin Osinbajo na bin sahun Buhari

  • Tsohon dan majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani ya mayar da martani kan jawabin da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi na kudurinsa na zama shugaban kasa
  • A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, 13 ga Afrilu, Sani ya bayyana cewa shi dai ba ya tafiyar da harkokin siyasa kamar gado
  • Ya kuma kara da cewa irin wannan yunkuri na 'yan takara yaudara ne da kokarin samun goyon bayan ubannin gidansu

A ranar Laraba, 13 ga wata ne, tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta 8, Shehu Sani, ya ce shi dai ya ki jinin siyasar ubangida.

Sani ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga jawabin da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Atiku ya kwadaitar da matasa, ya yi masu alkawari muddin ya samu mulki, su ma sun samu

Osinbajo dai shi ne dan takarar shugaban kasan da ya fito karara daga cikin 'yan takarar APC ya ce zai dora mulkinsa daga inda shugaba Buhari ya tsaya, lamarin da bai yiwa 'yan kasar da dama dadi ba.

Shehu Sani ga Osinbajo
Yaudara da neman goyon baya: Martanin Shehu Sani kan ikirarin Osinbajo na bin sahun Buhari | Hoto: Olubiyo Samuel
Asali: Original

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a yau Laraba, Shehu Sani ya tofa albarkacin bakinsa, inda ya bayyana cewa sam siyasar gado ba itace mafita ga kasar nan ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa a lokacin da 'yan ke irin wannan ikirari na bin sahun masu gidansu, duk kawai boyoyo ne da neman goyon bayan 'ubannin gidajensu'.

Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:

"Lokacin da 'yan takara suka ce za su ci gaba da ayyukan ubannin gidajensu, to wannan wata hanya ce ta yaudara don samun kwarin gwiwa da goyon bayan uban gidansu; a tsarin siyasa inda ake makahon biyayya ke da mahimmanci ga samun nasara. Babu batun da za a yi a siyasa ya zama zanen dutse."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Dattawan Arewa sun bukaci murabus din Buhari, sun sanar da dalilinsu

Shehu Sani dai ya saba martani kan 'yan siyasar kasar nan, musamman a inda suka yi kuskure ko kuma yake ganin ya kamata a jawo hankulansu.

Abin da ‘Yan Facebook da Twitter ke ta fada kan shirin takarar Osinbajo a zabe mai zuwa

A wani labarin, a wannan rahoto, mun tattaro abin da jama’a ke fada a dandalin sada zumunta a kan takarar mai girma mataimakin shugaban na Najeriya.

Ga na mu nan. Mu na nan! Shugaban kasar gobe. @ProfOsinbajo #Starboy #OsinbajoDeclares.

Haka dai 'yan Najeriya da dama suka dinga nuna ra'ayoyinsu ga fatan Osinbajo na gaje Buhari a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.