Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka hallaka wani, suka sace 'yarsa mai shekaru 15 a Zaria

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka hallaka wani, suka sace 'yarsa mai shekaru 15 a Zaria

  • Rahoto daga jihar Kaduna ya bayyana cewa, 'yan bindiga sun farmaki gidan wani mutum a Zaria, sun sace 'yarsa
  • Hakazalika, an ce sun harbe shi har lahira kafin daga bisani suka yi awon gaba da 'yarsa mai shekaru 15
  • An basu farmaki kowa ba, iyaka dai sun shiga gidan Alhaji Ardo sun hallaka shi sun yi tafiyarsu

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Dorayi da ke unguwar Dutsen Abba a karamar hukumar Zaria, inda suka kashe wani Alhaji Abdullahi Ardo tare da sace ‘yarsa mai shekaru 15 mai suna Mariya.

Wani ganau ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 2 na safe, inda suka tafi kai tsaye gidan marigayin, inji rahoton Daily Trust.

Yadda 'yan bindiga suka tafka barna a jihar Kaduna
Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka hallaka attajiri, suka sace 'yarsa mai shekaru 15 | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wani ganau ya ce:

“Daga nan ne suka tafi ba tare da kai hari a kan wani gida ko mutum ba. Muna jin sun zo ne musamman don daukar Alhaji Ardo, da suka yi yunkurin haka, watakila ya yi turjiya, shi ya sa suka harbe shi, sannan suka yi awon gaba da ‘yarsa.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun halaka basarake da wasu mutum 24, sun sace babura a Benue

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kauyen Dorayi na daya da cikin kauyukan da suka fuskanci hare-haren ‘yan bindiga da dama a baya bayan nan, inda aka sace mutane da dama, ciki har da hakimin kauyen.

A kauyen ne aka kama wasu sojoji da wani dan banga a lokacin da suke kan hanyarsu ta karbar kudin fansa ga hakimin kauyen.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ba.

Yadda aka kashe Sadiya da diyarta mai shekaru 4 a Kebbi sannan aka yanke wasu sassa na jikinsu

Rundunar yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da kisan wata mata da diyarta mai shekaru hudu a gidansu da ke Birnin Kebbi, babbar birnin jihar a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun dakile mota dauke da N100m kudin fansa za'a kaiwa yan bindiga

Premium Times ta rahoto cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun kashe Sadiya Idris mai shekaru 25 da diyarta Khadija a daren ranar Lahadi a gidanta da ke yankin Labana Rice Mills a titin Sani Abacha, Birnin Kebbi.

Yan sandan sun bayyana cewa ba a ga wasu sassa na jikin uwar da diyartata ba. An tsinci gawar tasu ne a safiyar Litinin.

Rundunar yan sandan ta kuma ce ana nan ana gudanar da bincike a kan al’amarin.

A halin da ake ciki, gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu, ya ziyarci iyalan mamatan domin yi masu ta’aziyya. Tuni aka binne uwar da diyar daidai da koyarwar addinin Musulunci.

Sai dai kuma, yayar marigayiya Sadiya, Hajiya Sahura Mukhtar ta bayyana cewa mijin marigayiyar wanda ya kasance tela ne ya bar gidansa da misalin karfe 1:00 na tsakar dare zuwa shagonsa sannan aka kashe matar tasa da misalin karfe 4:00 na asuba, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun kutsa har cikin gida sun kashe wani fitaccen Attajiri a Katsina da Azumi

Zamfara: 'Yan bindiga sun sace dalibai 5 na kwalejin lafiya da ke Tsafe

A wani labarin, 'yan bindiga sun kutsa wani yanki na garin Tsafe kuma sun sace dalibai biyar na kwalejin kiwon lafiya da fasaha da ke tsafe a jihar Zamfara. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, lamarin ya faru ne a sa'o'in farko na ranar Laraba.

Wata majiya ta sanar da cewa miyagun 'yan bindiga dauke da miyagun makamai ne suka dira gidan daliban wanda yake wajen makaranta.

Ya ce 'yan bindiga ba za su taba samun damar shiga makarantar ba saboda jami'an tsaron da ke kofar shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.