Buhari: Hukuma Ba Za Ta Bar Waɗanda Suka Kai Harin Filato Ba, Za Su Gane Kurensu
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnati ba za ta kyale duk wadanda ke da alhakin kai farmakin Kanam da Wase da ke Jihar Filato ba
- Shugaban kasa ya sha wannan alwashin ne a wata takarda wacce ya saki a ranar Talata ta hadiminsa na harkar watsa labarai, Garba Shehu
- A takardar, Buhari ya ce babu wanda zai yafe musu kuma ya bai wa jami’an tsaro umarnin zakulo su sannan su yi gaggawar dawo da zaman lafiya yankin
Filato - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alawadai da munanan hare-haren da wasu ‘yan ta’adda suka kai Kanam da Wase da ke Jihar Filato kuma ya ce duk wadanda ke da alhakin kai farmakin ba za su tsira daga fushin hukuma ba.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ta wata takarda wacce ya saki ta hadiminsa na harkar watsa labarai, Garba Shehu a ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.
Buhari ya bayar da umarni ga jami’an tsaro inda ya ce kada su kyale su sannan su yi aiki da gwamnatin jihar wurin gano su da kuma gabatar da su don a yanke musu hukunci.
Shugaban kasa ya lashi takobin hukunta duk wadanda suke da alhakin kai harin
Premium Times ta bayyana yadda Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga wadanda harin ya shafa inda ya ce za a yi iyakar kokarin ganin an dawo da zaman lafiya a jihar da kasar baki daya.
Kamar yadda ya ce:
“Na yi wa jama’an kasar nan, musamman mutanen Jihar Filato alkawarin cewa sai an fallasa wadanda suka kai farmakin nan, masu daukar nauyinsu da masu mara musu baya.
“Za a yi hakan ne don doka ta yi aiki akansu. Ba za a taba yafe musu ba.”
Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed
A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.
Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.
Asali: Legit.ng