Ramadan: Magidanci ya lakada wa matarsa mai ciki mugun duka kan abincin Sahur
- Wani mutumi mai matsakaicin shekaru ya nada wa matarsa mai ciki dukan kawo wuka, saboda ta gaza girka masa abincin Sahur
- Ganau ya bayyana yadda mutumin ke da dabi'ar dukan matarsa a kan dan kankanin abu idan sun samu sabani, ba tare da daga mata kafa ba
- Wannan karon bai yi dubi da lalurar da take dauke da shi ba na juna biyun dansu na biyu, ya fara jibgarta ba kakkautawa, inda ta dauki awanni tana kururuwa kafin ta tsere
Ibadan - Wani mutum mai matsakaicin shekaru mai suna Taofeek Gbolagade, a safiyar Talata, ya nadawa matarsa mai juna biyu, wacce aka boye sunanta, dukan kawo wuka saboda ta gaza girka masa abincin sahur.
Vanguard ta gano yadda lamarin ya auku misalin karfe 4:00 na asuba a gidansu dake cikin rukunnan gidajen Ogbere cikin Ibadan na jihar Oyo.
Wani ganau ya ce: "Wannan mutumin ya saba dukan matarsa a kan duk wani karamin sabanin da suka samu. Yau dai na fahimci abunda ya faru. Shi musulmi ne, saboda haka ina tunanin sun yi sa-in-sa a kan abincin Sahur.
"Mutumin nan bai damu da tana dauke da juna biyun 'dansu na biyu ba, ya fara jibgarta. Ta dau tsawon awanni tana kururuwa kafin ta samu damar tserewa gidan iyayenta. Gbolagade ya ranta a na kare bayan jami'an tsaro sun fara nemansa ruwa a jallo."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin 'yan sandan jihar, Adewale Osifeso ya ce, a halin yanzu na bincikar lamarin, sannan za'a sanar da cikkaken bayani idan bukatar hakan ta taso, Punch ta ruwaito.
Na yiwa mijina dukan tsiya ne saboda yana raina mini wayo da yawa - Matar aure ta sanar da kotu
A wani labari na daban, a ranar Talatar da ta gabata ne wata karamar 'yar kasuwa, mai suna Damilola Osilulu, ta sanar da kotun Ile-Tuntum dake Ibadan, cewa ta yiwa mijinta mai suna Akinkunmi duka ne saboda yana raina mata wayo yana gaya mata abinda za tayi a rayuwarta.
Da take tabbatar da faruwar lamarin a gaban alkalin kotun, Cif Henry Agbaje, ta zargi cewa mijinta yana da korafi da yawa sannan kuma koda yaushe yana yawan tambayar abubuwa.
Asali: Legit.ng