Na yiwa mijina dukan tsiya ne saboda yana raina mini wayo da yawa - Matar aure ta sanar da kotu

Na yiwa mijina dukan tsiya ne saboda yana raina mini wayo da yawa - Matar aure ta sanar da kotu

- Wata matar aure ta bayyana dalilin da ya sanya ta yiwa mijinta dukan tsiya

- Ta sanar da kotu cewa mijin yana raina mata hankali sosai ne, ita kuma ta gaji da abinda yake yi mata shi yasa ta zane shi

- Matar ta bayyana hakane a gaban alkalin wata kotu dake garin Ibadan babban birnin jihar Oyo

A ranar Talatar da ta gabata ne wata karamar 'yar kasuwa, mai suna Damilola Osilulu, ta sanar da kotun Ile-Tuntum dake Ibadan, cewa ta yiwa mijinta mai suna Akinkunmi duka ne saboda yana raina mata wayo yana gaya mata abinda za tayi a rayuwarta.

Da take tabbatar da faruwar lamarin a gaban alkalin kotun, Cif Henry Agbaje, ta zargi cewa mijinta yana da korafi da yawa sannan kuma koda yaushe yana yawan tambayar abubuwa.

Na yiwa mijina dukan tsiya ne saboda yana raina mini wayo da yawa - Matar aure ta sanar da kotu
Na yiwa mijina dukan tsiya ne saboda yana raina mini wayo da yawa - Matar aure ta sanar da kotu
Asali: Facebook

"A lokuta da dama Akinkunmi yana yawan sanyani nayi wasu abubuwa na rashin hankali ni kuma bana bin umarnin shi.

"Haka kuma, duk lokacin da ya tambaye ni abu ina kokari naga na biya masa bukatarsa.

"Dana gaji da rainin hankalinshi ne yasa nayi masa dukan tsiya, saboda yana ji a ranshi shine miji dan haka dole abinda yace dole za ayi," cewar Damilola.

Sai dai da aka bukaci jin ta bakinshi Akinkunmi ya bukaci a raba auren shi da matar tashi.

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda aka kama wata budurwa 'yar aiki tana zubawa uwar dakinta fiya-fiya a cikin ruwan sha

"Ranka ya dade, bani da ikon yin wani katabus a cikin gidana sai ta kalubalance ni.

"Idan na bukaci tayi wani, sai taki yi a karshe ma ta fara kawo mini hari.

"Wannan ya sanya mutane suke ta zuwa gidanmu domin daidaita tsakaninmu.

"Allah ne kadai yasan mai zai faru da ace na biye ta a lokacin da ta nemi fada dani kwanan nan.

"Na gaji da cin mutuncinta, bayan haka bata kula da yaron mu mai shekaru uku a duniya," Akinkunmi ya ce.

A yayin da yake bayani alkalin kotun ya bukaci ma'auratan da su kara hakuri. Ya bukaci 'yan uwan ma'auratan akan su yi kokari wajen daidaita su.

A karshe alkalin ya daga sauraron karar zuwa ranar 31 ga watan Agustan nan. (NAN)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel