N225bn: Yayin da ake fama da rashin wuta, Najeriya ta wadatar da kasashen waje 3
- Wani sabon rahoto ya nuna cewa gwamnatin Najeriya a shekarar 2021 ta samu sama da Naira biliyan 225 daga wutar lantarki kasata hanyar sayarwa kasashen waje
- Babban Bankin Najeriya ne ya bayar da wannan bayanin yayin da yake lura da cewa an samu raguwar kudaden na shekarar 2021 idan aka kwatanta da na 2020
- Nijar, Benin, da Togo sune manyan kasashe uku da ke sayen wutar lantarki daga gwamnatin tarayya
Duk da rashin samar da wutar lantarki a kasar nan, babban bankin Najeriya ya bayar da rahoton cewa fitar da wutar lantarki zuwa kasashen da ke makwabtaka da Najeriya ya samar da kudaden shiga na Naira biliyan 29.95 (dala miliyan 72) a 2021.
Wannan ya biyo bayan dala miliyan 84.26 da aka samu a 2020 da dala miliyan 142.3 a shekarar 2019.
A cikin shekaru biyar da suka gabata, jimlar bayanai na CBN sun nuna cewa Najeriya ta samu dalar Amurka miliyan 543.11 (sama da N225bn) daga wutar lantarki da ake fitarwa zuwa kasashen makwabta kamar Nijar, Benin, da Jamhuriyar Togo, inji rahoton Nairametrics.
Matsalar wuta a Najeriya
Bayyana kudaden shigar da gwamnatin tarayya ke samu daga fitar da wutar lantarki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tasgaro a fannin wutar lantarki a kasar sakamakon rugujewar turken wuta da ake yawan samu a kasar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cikin wata guda, an tilasta wa kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) yin bayani tare da ba 'yan Najeriya hakuri kan matsalar wuta har sau uku a lokuta daban-daban.
Na baya-bayan nan shine na ranar Asabar, 9 ga Afrilu, 2022. A ranar 8 ga Maris, 2022 daga shafin Twitter NA Ikeja Electric, an tilas ya sanar da cewa:
"Muna sanar da ku cewa matsalar da kuke fuskanta a halin yanzu ya samo asali ne sakamakon rushewar tsarin wutar lantari na kasa wanda ya faru a yau da karfe 17:10 na safe kuma hakan ya shafi tashoshin wutan mu."
Buhari ya bada izinin fitar da ton 40,000 na kayan hatsi daga rumbun gwamnati don bikin Easter da Azumi
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin fitar da kayan hatsi ton 40,000 daga rumbun kayan masarufin gwamnati don taimakawa talakawa wajen murnin bikin Easter, azumi da Sallah.
Ministan noma da raya karkara, Muhammad Mahmoud, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da shugaban kasa.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya bayyana cewa Mahmoud ya gaba da Buhari ne ranar Talata, 12 ga Afrilu, 2022.
Asali: Legit.ng