Dan baiwa: Bidiyon mai shekaru 8 da ya haddace Al-Qur'ani da wasu littatafai a Zaria

Dan baiwa: Bidiyon mai shekaru 8 da ya haddace Al-Qur'ani da wasu littatafai a Zaria

  • Wani bidiyon da aka yada na wani matashin da ya haddace Qur'ani ya ba da mamaki, inda ya bayyana kadan daga tarihin rayuwarsa
  • Ya bayyana cewa, shi dai ya fara haddar Qur'ani ne tun yana da shekaru uku a rayuwarsa, ya kammala yana da shekaru takwas
  • Mun samo bidiyon da aka yada, inda ake hira dashi cikin harshen Turanci kana yana sirkawa da Larabci

Kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa, amma baiwar Qur'ani tana daga cikin kyauta mafi girma daga wurin Allah.

Wani matashi mai shekaru 8 ya haddace Qur'ani da wasu littafan, inda aka ga yana magana da yaren Turanci kana yana zagaye da littafai da ke nuna alamar daga gidan ilimi yake kuma tabbas ya karantu.

Kara karanta wannan

Ni wai mai digiri: Na yi danasanin rashin iya sana'ar hannu, da yanzu na kudance a Kanada

A bidiyon da jaridar Daily Trust ta yada, an ga yana bayani kan kyauta da albarkar da Allah ya zuba masa a rayuwarsa, inda yace karatu shi ne komai na burin rayuwarsa.

Matashin da ya haddace Qur'ani
Dan baiwa: Bidiyon mai shekaru 8 da ya haddace Al-Qur'ani da wasu littatafai a Zaria | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Daga cikin bidiyo, ya bayyana cewa, ya fara haddace Qur'ani tun yana da shelaru uku a duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buri na na zama babban Malami, inji Muhammad Shamsudden

Da yake godewa Allah bisa ni'imar da ya yi masa, ya bayyana cewa, yana koyi da manyan malamai domin zama mai irin halinsu, ko da kuma ba zai zama su ba.

Ya ce, an yi malamai a duniya da suka haddace Qur'ani a kananan shekaru, inda ya ambaci sunayen Imam Shafi' da wasu malamai da dama.

Ya kuma ce, babban farin cikin rayuwarsa shine, kasancewa ya tashi da kaunar manzon Allah SAW, inda yace idan ya tuna hakan yana bashi farin ciki mai tarin yawa.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Bidiyon busasshen tsohon da mutuwa ta mance dashi ya girgiza intanet

Kalli cikakken bidiyon:

Sadu da matashiyar da ta rubuta Al-Qur’ani mai girma cikin watanni uku

A wani labarin daban, Sumayyah Shuaibu Salisu ta kasance matashiya yar shekara 18 wacce ta haddace da kuma iya rubuta Al-Qur’ani mai girma da ka a Zaria.

Sumayya wacce aka haifa a garin Jega da ke jihar Kebbi, ta kasance diya ta uku a wajen Shehin malamin nan na Najeriya kuma mazaunin kasar Saudiyya, Shuaibu Salisu Zaria, wanda ya dawo kasar bayan kammala digirinsa na biyu a jami’ar Madina da ke Saudiya.

A wata hira da tayi da jaridar Daily Trust, Sumayyah ta ce:

“Zuwa yanzu, na rubuta cikakken Al-Qur’ani mai tsarki da hannuna ba tare da wani ya nuna mun ko na kwafa daga wani littafi ba cikin watanni uku; kuma a yanzu ina rubuta na biyu. Idan Allah ya yarda, zan kammala shi shima cikin wata daya ko fiye da haka.

Kara karanta wannan

Mubarak Bala: Martanin 'yan Najeriya kan hukuncin shekaru 24 da kotu ta yanke wa mulhidi

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.