Shirin 2023: Bayan ganawa da gwamnoni, Osinbajo ya gayyaci 'yan majalisun APC
- Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya sake gayyatar tawagar 'yan jam'iyyar APC zuwa taron buda baki
- A wannan karon, ya tura wasikar gayyata ne ga 'yan majalisun tarayya da aka zaba a jam'iyyar APC
- Rahotanni da ke fitowa daga majalisar sun bayyana cewa, gobe Laraba ne Osinbajo zai gana da jiga-jigan siyasar
Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo zai gana da mambobin jam’iyyar APC a majalisar wakilai ta Najeriya, inji rahoton Punch.
Osinbajo ya gayyaci ‘yan majalisun na jam’iyyar APC ne zuwa dakin taro na Banquet dake fadar shugaban kasa domin buda bakin azumin watan Ramadan a ranar Laraba.
Mataimakin kakakin majalisar, Ahmed Wase ne ya karanta wasikar da mataimakin shugaban kasa ya aika ga kungiyar wakilan na APC a wajen bude zaman majalisar a yau Talata.
Gayyatar Osinbajo ta zo ne kasa da sa’o’i 48 bayan da ya karbi bakuncin gwamnonin jam’iyyar APC zuwa buda baki a daren Lahadi domin neman goyon bayansu kan aniyarsa ta takarar shugaban kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da sanyin safiyar ranar Litinin ne mataimakin shugaban kasar ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a babban zabe na 2023.
Mataimakin shugaban kasar wanda ya bayyana aniyar sa a wani taro da gwamnonin APC, ya ce yana son daurawa nasarorin shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa gaba, inda ya kara da cewa ya fahimci abubuwan da 'yan Najeriya ke bukata.
Ya batun 'yan PDP a majalisa?
A bangare guda, Udom Emmanuel, gwamnan jihar Akwa Ibom, ya bukaci ganawa da mambobin jam’iyyar PDP a zauren majalisar.
A cewar wasikar da Wase ya karanta, an shirya taron ne da karfe 8 na dare a ranar Talata.
Jaridar TheCable ta ruwaito cewa Brekete Family, shirin talabijin da rediyo da ke mai da hankali kan batutuwan kare hakkin dan adam, ya saya wa Emmanuel fom din takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP.
An mika wa gwamnan fom din ne a ranar Juma’a a gidan gwamnati da ke Uyo lokacin da tawagar kungiyar ta kai masa ziyara.
Osinbajo zai yi buɗe baki tare da Sanatocin Jam'iyyar APC yau
A wani labarin, mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a ranar Talata, zai karɓi baƙuncin Sanatocin jam'iyya mai mulki APC domin buɗa baki na Azumin yau.
Wannan na ƙunshe ne a wata wasiƙar gayyata da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya karanta a zauren majalisa, kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto.
Wasikar gayyar shan ruwan na ɗauke da sa hannun jagoran majalisar dattawa, Yahaya Abdullahi.
Asali: Legit.ng