Yanzu-yanzu: Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Kyari sun yi murabus daga majalisar dattawa

Yanzu-yanzu: Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Kyari sun yi murabus daga majalisar dattawa

  • Bayan kimanin makonni uku da zama shugaban jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ya ajiye kujerarsa ta Sanata
  • Sanata Abdullahi Adamu ya kwashe sama da shekaru goma a majalisar dattawar tarayya
  • Wannan na faruwa ne lokacin da Lauyoyi ke munakasha kan shin wajibi ne ya yi murabus ko zai iya rike kujerun biyu

Birnin tarayya Abuja - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Abdullahi Adamu, ya yi murabus daga majalisar dattawar tarayya.

An zabi Abdullahi Adamu ne matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC a ranar 26 ga Maris yayin taron gangamin jam'iyyar.

Sanata Adamu ya kasance mai wakiltar Nasarawa ta yamma a majalisar.

Ya shiga majalisa tun shekarar 2011 har ila yau da yayi murabus.

Sanata Abdullahi Adamu
Yanzu-yanzu: Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Kyari sun yi murabus daga majalisar dattawa Hoto: @APCNigeria
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Bayan ganawa da gwamnoni, Osinbajo ya gayyaci 'yan majalisun APC

Hakazalika mataimakin shugaban jam'iyyar APC mai wakiltan Arewa, Sanata Abubakar Kyari, ya yi murabus.

Gabanin murabus dinsa, Sanata Kyari ya wakilci mazabar Borno ta Arewa.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya sanar da hakan a wasikun da ya karanta ranar Talata.

Wajibi ne APC ta lashe zabe a 2023 saboda ban taba rashin nasara ba, Abdullahi Adamu

Shugaban uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Sanata Abdullahi Adamu ya lashi takobin tabbatar da cewa jam'iyyarsa ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Abdullahi Adamu, wanda tsohon Gwamna ne kuma Sanata, ya ce bai taba rashin nasara a wani abu da ya jagoranta ba kuma a wannan ma ba zai fadi ba.

Adamu ya bayyana hakan karshen makon da ya gabata a hira da manema labarai a gidansa na Abuja.

Yace ko kadan ba zasu yarda su fadi ba saboda wannan ne aikinsu na farko kuma abinda zasu yi shine dakatar da duk wani abinda zai sa suyi rashin nasara.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tsohon hadimin shugabannin Najeriya biyu ya rigamu gidan gaskiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel