Kuyi hattara, zamu diro kanku kamar yadda mukewa Ukraine: Rasha ta gargadi Finland da Sweden

Kuyi hattara, zamu diro kanku kamar yadda mukewa Ukraine: Rasha ta gargadi Finland da Sweden

  • Rasha ta gargadi kasashen Sweden da Finland kada su yi abinda Ukraine tayi kokarin yi gudun abin ka iya biyowa baya
  • NATO wata kungiyar kasashen 30 (Turai 28 da Amurka da Kanada) ne da aka kafa na hada karfi da karfe
  • Wannan shine babban dalilin da yasa kasar Rasha ta fara kai wadannan hare-hare Ukraine

Moscow - Gwamnatin kasar Rasha ta gargadi kasashen Finland da Sweden kan shirin shiga kungiyar NATO da sukeyi, tace ba zai amfanar da Turai da komai ba.

Dmitry Peskov, Mai magana da yawun shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, yace shiga NATO tamkar fito-na-fito ne da kasar Rasha, rahoton BBC.

Jami'an kasar Amurka sun ce kasashen dake makwabtaka da Rasha zasu fara shiga kungiyar NATO daga watar Yuni.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta gurfanar da Janar din Sojan Bogi kan damfarar miliyoyi

Jami'an ma'aikatar wajen Amurka a makon da ya gabata sunce ana tattaunawa tsakanin shugabannin NATO da ministocin wajen kasar Finland da Sweden.

Shugaban Rasha
Kuyi hattara, zamu diro kanku kamar yadda mukewa Ukraine: Rasha ta gargadi Finland da Sweden
Asali: Getty Images

Yakin Rasha da Ukraine

Zaku tuna cewa a ranar Alhamis, 24 ga watan Febrairu, kasar Rasha ta fara kai hare-hare cikin Ukraine da nufin kwace kasar daga hannun Vlodomyr Zelensky, Shugaban kasar.

Hakan ya biyo bayan gargadin da Rasha ta yiwa Ukraine na kokarin shiga kungiyar NATO, wacce ke karkashin jagorancin Amurka amma shugaban Ukraine Zelensky ya lashi takobin cewa lallai sai ya shiga kungiyar.

Watanni biyu kenan har yanzu ana artabu tsakanin Rasha da Ukraine kuma dubunnan mutane sun rasa rayukansu.

Menene kungiyar NATO

Kungiyar NATO (North Atlantic Treaty Organization) wata kungiyar kasashen 30 (Turai 28 da Amurka da Kanada) ne da aka kafa na hada karfi da karfe.

Kara karanta wannan

Najeriya ce ta 4 cikin jerin kasashen duniya da aka fi cin Karnuka, Sabon Bincike

An kafa kungiyar bayan yakin duniya na biyu kuma an kafa ta ranar 4 ga watan Afrilu, 1949.

Duk mamban kungiyar da wani ya kaiwa hari ya tono tsokanar sauran kasahen talatin.

Me yasa Rasha ba ta son makwabtanta su shiga NATO

Shugaban Rasha, Putin, ya bayyana cewa ba shi da niyyar kai hari kasashen dake makwabtaka da kasarsa amma kada su shiga kungiyar NATO.

Rasha tace inda ta amince suka shiga NATO, makiyanta irinsu Amurka dake kungiyar NATO zasu kusanto da makamansu kusa da ita kuma zasu iya kai mata hari a koda yaushe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel