Mun saduda, mun hakura da shiga kungiyar NATO: Shugaban kasar Ukraine

Mun saduda, mun hakura da shiga kungiyar NATO: Shugaban kasar Ukraine

  • Volodymyr Zelensky bayan kusan wata guda ana yakar al'ummarsa ya ce gwamma su hakura da lamarin shiga NATO
  • NATO wata kungiyar kasashen 30 (Turai 28 da Amurka da Kanada) ne da aka kafa na hada karfi da karfe
  • Wannan shine babban dalilin da yasa kasar Rasha ta fara kai wadannan hare-hare Ukraine

Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky , a ranar Talata ya bayyana cewa kasarsa ta hakura da shiga cikin kungiyar NATO, babban dalilin da yasa Rasha ta fara yakin nan.

A hirar da yayi da rundunar Sojin gaggawa karkashin Birtaniya, Zelensky yace da alamun zasu hakura tunda an fada musu ba zasu iya shiga ba, rahoton Aljazeera.

Yace:

"Ukraine ba mambar NATO bace. Mun san da haka. An dade ana fada mana zamu iya shiga, amma kuma ana fada mana yanzu ba zamu iya shiga. Wannan shine gaskiyar lamari."

Kara karanta wannan

Yakin Rasha da Ukraniya: An kashe yan jaridan Fox News biyu, an cirewa daya kafa

"Na ji dadi yanzu mutanenmu sun fahimci hakan kuma sun dogara da kansu da masu taimaka mana"

Shugaban kasar Ukraine
Mun saduda, muna fasa shiga kungiyar NATO: Shugaban kasar Ukraine Hoto
Asali: Facebook

A ranar Alhamis, 24 ga watan Febrairu, kasar Rasha ta fara kai hare-hare cikin Ukraine da nufin kwace kasar daga hannun Vlodomyr Zelensky, Shugaban kasar.

Hakan ya biyo bayan gargadin da Rasha ta yiwa Ukraine na kokarin da take na shiga kungiyar NATO, wacce ke karkashin jagorancin Amurka.

Amma Zelensky ya lashi takobin cewa lallai sai ya shiga kungiyar.

Kungiyar NATO (North Atlantic Treaty Organization) wata kungiyar kasashen 30 (Turai 28 da Amurka da Kanada) ne da aka kafa na hada karfi da karfe.

An kafa kungiyar bayan yakin duniya na biyu kuma an kafa ta ranar 4 ga watab Afrilu, 1949.

Duk mamban kungiyar da wani ya kaiwa hari ya tono tsokanar sauran kasahen talatin.

Kara karanta wannan

Karar kwana: An shiga jimami yayin da tsohon Sanatan Najeriya ya rasu a asibitin Landan

An kashe yan jaridan Fox News biyu, an cirewa daya kafa

Dan jaridan tashar Fox News dake Amurka, Benjamin Hall, ya rasa kafarsa guda yayinda aka bude musu wuta lokacin da suke daukan rahoto kan yakin dake gudana a Ukraine.

Anton Gerashchenko, mai baiwa Ministan harkokin cikin gidan a kasar Ukraine, ya bayyana hakan ranar Talata a shafinsa na Telegram.

Yace an kwantar da dan jaridan a asibiti bayan budewa motarsu wuta tare da abokan aikinsa kuma an kashe biyu cikinsu a Kyiv.

Asali: Legit.ng

Online view pixel