Najeriya ce ta 4 cikin jerin kasashen duniya da aka fi cin Karnuka, Sabon Bincike

Najeriya ce ta 4 cikin jerin kasashen duniya da aka fi cin Karnuka, Sabon Bincike

Kasar Vietnam, Sin da Najeriya ne kasashe uku a duniya dake sama wajen adadin masu cin karnuka a duniya.

Wannan na kunshe cikin sabon binciken da wani mai bahasi kan harkan karnuka, Matthew Nash, ya saki inda ya nuna kasashen da karnuka ke da gata da kasashen da basu da gata.

Kasashe da dama irinsu Najeriya na cikin kasashe 10 na farko da karnuka basu da gata dubi ga yadda ake kasheshu don sanwa.

Mr Nash ya bayyana cewa ya yi amfani da wasu ka'idoji bakwai wajen tantance kasashe 51 da ke da karnuka ke da gata, rahoton The Swiftest.

Wadannan ka'idoji sun hada da dokokin kare hakkin dabbobi, gidajen hutu masu yarda a shiga da karnuka, yawan Likitocin dabbobi, cutar Rabies, kyawun zama da dabbobi da jin dadin dabbobi.

Kara karanta wannan

Buhari ya rufe iyaka: Kwastam sun kama tirelolin shinkafar waje 11 da lita 82,700 na fetur

Najeriya ce ta 4 cikin jerin kasashen duniya da aka fi cin Karnuka, Sabon Bincike
Najeriya ce ta 4 cikin jerin kasashen duniya da aka fi cin Karnuka, Sabon Bincike Hoto: theswiftest.com/dog-friendly-countries
Asali: UGC

An saki rahoton binciken ne ranar 25 ga Maris, 2022.

Najeriya ce kasa ta 45 cikin kasashe 51 da kare ke da gata.

Kasashe irinsu Italiya Nu zilan, Faransa, Birtaniya da Jamus ne kasashe biyar da karnuka suka fi gata.

Sun cire tuta ne saboda kasashen sun kafa dokokin kare hakkin dabbobi da kuma iya zamantakewa da su.

Mafarauta a jihar Borno sun kashe katon Zaki a garin Konduga

Shugaban Hukumar harkokin gandun daji na ma'aikatar yanayi a jihar Borno, Peter Ayuba, ya tabbatar da kisan Zaki da mafarauta sukayi a karamar hukumar Konduga dake jihar.

Ayuba, ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ranar Talata a Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.

Ya ce da yiwuwan Zaki ya shiga jihar ne daga gidan ajiye namomin daji a Kamaru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel