Innalillahi wa’inna illahi raji’un: Allah ya yiwa sajan Funtua wanda harin jirgin kasa ya cika da shi rasuwa

Innalillahi wa’inna illahi raji’un: Allah ya yiwa sajan Funtua wanda harin jirgin kasa ya cika da shi rasuwa

  • Allah ya yiwa Sajan Muhammad Haruna Funtua, wanda harin jirgin kasan Kaduna ya ritsa da shi, rasuwa sanadiyar harbin bindiga da ya same shi a kai da kirjinsa
  • Sajan Funtua na daya daga cikin fasinjojin da hukumomin tsaro suka ceto daga hannun yan bindigar da suka dasa bam a hanyar jirgin kasan a makon da ya gabata
  • Marigayin ya rasu ne a ranar Talatar da ta gabata a mahaifarsa ta Funtua da ke jihar Katsina inda aka kai shi domin yin jinya

Daya daga cikin mutanen da harin jirgin kasa ya ritsa da su a kwanan nan, Sajan Muhammad Haruna Funtua, ya kwanta dama. Marigayi tsohon sojan ya rasu ne sakamakon wasu raunuka da ya samu a yayin harin.

Kara karanta wannan

Korarren Liman Nuru Khalid: A da mimbarin masallacin Apo ne cibiyar kamfen din Buhari

Marigayin wanda aka harba a kai da kirji yayin harin na jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a makon da ya gabata na daga cikin wadanda jami’an tsaro suka ceto,rahoton Nigerian Tribune.

Innalillahi wa’inna illahi raji’un: Allah ya yiwa sajan Funtua wanda harin jirgin kasa ya cika da shi rasuwa
Innalillahi wa’inna illahi raji’un: Allah ya yiwa sajan Funtua wanda harin jirgin kasa ya cika da shi rasuwa Hoto: Nigerian Tribune
Asali: UGC

An tattaro cewa daga baya an kwashe shi zuwa mahaifarsa ta Funtua domin ci gaba da samun kulawar likitoci inda a nan ne ya amsa kiran mahaliccinsa.

Wani majiya da ya bayyana kansa a matsayin Mallam Idris ya bayyana cewa tsohon jami’in tsaron ya rasu ne a ranar Talata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Ya sha gwagwarmaya amma abun bakin ciki, bai kai laraba ba sannan ya mutu.
“Muna addu’an Allah ya ji kansa ya saka masa da Aljannatul Firdausi.”

Shafin Linda Ikeji ya kuma rahoto cewa marigayi Haruna na daga cikin dattawan garinsa da ke tallafawa yan sa-kai.

Kara karanta wannan

Dattijon arewa ya yi fallasa, ya sanar da abinda Gumi ya fadi wa 'yan bindigan daji

‘Yan bindiga za su ‘kashe’ fasinjojin jirgin kasa, idan Gwamnati ta gaza biya masu bukata

A halin da ake ciki, mun ji cewa yan bindigan da suka dasa bam a hanyar jirgin kasa, su ka yi awon-gaba da Bayin Allah su na barazanar cewa za su kashe mutanen da ke hannunsu.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 6 ga watan Afrilu 2022, inda aka ji cewa wadannan ‘yan ta’addan su na gargadin gwamnatin tarayya.

A wani gajeren faifen bidiyo da ya bayyana a jiya, an ji ‘yan bindigan su na cewa ba kudi ne a gabansu ba. Akasin yadda aka saba ji idan an dauke mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel