Batun rashin tsaro: Tsohon ministan Buhari ya yiwa shugaban kasar wankin babban bargo
- Barista Solomon Dalung, tsohon ministan matasa da wasanni, ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda matsalar rashin tsaro
- Dalung ya ce tsohon ubangidan nasa ya gaza cika alkawaran da ya daukarwa yan Najeriya na kare rayuka da dukiyoyinsu
- Tsohon ministan ya kuma bayyana cewa Buhari ya basu kunya saboda duk da kasancewarsa Janar gashi suna raba iko da Bello Turji wanda ya addabi arewa maso yamma
Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gazawa yan Najeriya sannan cewa ya baiwa mutane da dama kunya ciki harda shi saboda ya kasa magance matsalar rashin tsaro a kasar.
Dalung ya bayyana hakan ne a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 10 ga watan Maris.
Tsohon ministan ya kuma koka kan cewa shugaban kasar na raba iko tare da kasurgumin shugaban yan bindiga na arewa maso yamma, Bello Turji da kuma mayakan ISWAP sakamakon gazawarsa wajen magance rashin tsaro.
Har ila yau, Dalung ya bayyana cewa ya shiga sahun sauran yan Najeriya wajen yiwa APC da shugaba Buhari kamfen saboda rashin jin dadin yadda gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ke tafiyar da matsalar tsaro a kasar a wancan lokacin.
Ya bayyana cewa ya gana da tsohon shugaban kasar sannan ya bashi shawara kan yadda zai magance hauhawan rashin tsaro a lokacin, amma aka yi watsi da shawararsa.
Ya ce:
“A karkashin Goodluck Jonathan an yi ta kashe mutane a Filato, ana tayar da wuraren bauta, ofishoshin gwamnati da kamfanoni da bama-bamai, ana ta kashe-kashe, fille kawuna da sace mata da yaran makaranta a arewa maso gabashin Najeriya.
“Martanin da gwamnatin Jonathan ta bayar kan wannan ta’asa ba na hankali bane kuma sau da yawa ba wanda ya dace ba kamar yadda ake tsammani daga gwamnati.
“Na jagoranci tafiyar “Chanji” kan gwamnatin bayan ganawa da Shugaba Jonathan sau da dama tare da bashi shawara kan mafita wanda ba wai an yi watsi bane da shi kawai illa an dauke ni a matsayin makiyin kasa tare da kokarin daukar rayuwata.”
Sai dai Dalung, wanda ya yi ikirarin cewa ya zama abun ki a al’umman kirista saboda shiga kamfen din adawa da gwamnatin Jonathan ya ce koda dai Buhari ya samu wasu nasarori a bangaren samar da ababen rayuwa, amma ya kasa cika alkawarinsa na kare rayuka da dukiyar yan Najeriya, daya daga cikin muhimman tsare-tsaren da suka sa aka zabe shi.
Ya kara da cewa:
“Shugaban kasa Muhammadu Buhari dan Najeriya ne mai nufin kasar da alkhairi kuma yana da rikon amana, ina son shi sosai amma rikon amana kadai bai isaba a wannan yanayi, magana ta gaskiya, Baba Buhari ya gazawa yan Najeriya kuma y aba mutane da yawa kunya ciki harda ni.
“Shugaba Buhari ya yi kokari wajen samar da ababen more rayuwa, amma a karkashin kulawarsa ‘yan fashi da masu ta’addanci na ci gaba da bunkasa ba tare da wani hukunci ba, kuma shi din Janar ne, tsohon shugaban kasa a mulkin soja kuma kwamandan rundunar soji. Me yasa shugaban kasa zai raba mulki tare da Bello Turji da ISWAP?
"Dole ne ka saurari muryar hankali, a gyara tsarin tsaro, a murkushe yan ta’adda kafin ka bar mulki idan ba haka ba mu magoya bayan ka ba za mu samu damar kare mutuncin ka ba" Wannan ita ce shawarata ta karshe ga Shugaba Muhammadu Buhari a ranar 3 ga Maris 2020. Ban sake samun damar tattaunawa da shi ba tun daga lokacin duk da shan neman yin hakan.
“Ba zan yi kasa a gwiwa ba wajen magana kan rashin adalci da rashin tsaro ba saboda “idan har yanzu ina neman burge mutane, toh ban cancanci zama dan aiken almasihu ba.”
Matsalolin da Najeriya ke fuskanta alamun daukaka ne, In ji dan majalisa daga arewa
A wani labarin, dan majalisar dokokin tarayya daga jihar Sokoto, Ibrahim Almustapha, ya bayyana cewa matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu alamu ne na daukaka, cewa kasar na da ikon za ta iya tsallake su.
Almustapha wanda ke wakiltan mazabar Wurno/Rabah na jihar Sokoto a majalisar wakilai, ya bayyana hakan ne da yake zantawa da manema labarai a garin Sokoto a ranar Lahadi, Premium Times ta rahoto.
Asali: Legit.ng