2023: 'Ya'yan gwamnoni da tsoffin gwamnoni 5 da ke haramar hayewa madafun iko

2023: 'Ya'yan gwamnoni da tsoffin gwamnoni 5 da ke haramar hayewa madafun iko

Najeriya - A yayin da zaben 2023 ke gabatowa, 'ya'yan wasu gwamnoni da tsoffin gwamnoni sun bayyana burinsu na fitowa takarar kujerun siyasa daban-daban.

A yayin da wasu ke son haye madafun iko don zama gwamnoni kamar iyayensu, wasu kuwa hararo majalisar wakilai suke yi karkashin jam'iyyun siyasar mahaifan nasu.

2023: 'Ya'yan fitattun 'yan siyasa 5 da ke hararo kujerun siyasa a arewacin Najeriya
2023: 'Ya'yan fitattun 'yan siyasa 5 da ke hararo kujerun siyasa a arewacin Najeriya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daga cikin 'ya'yan 'yan siyasan arewa da suka bayyana burinsu akwai dan gwamnan jihar Kaduna, dan tsohon gwamnan Jigawa, dan tsohon gwamnan Sokoto da kuma dan tsohon gwamnan Bauchi.

Yayin da wasu ke cewa 'ya'yan wadannan 'yan siyasa suna da damar takara a matsayinsu na 'yan kasa, wasu kuwa na nuna cewa gwamnonin ne ke hankada 'ya'yansu zuwa ofisoshin mulkar jama'a domin su handami nasu rabon.

Ga jerin sunaye da mukaman da 'ya'yan 'yan siyasan ke hararowa:

Kara karanta wannan

Bayan ya koma PDP, Labaran Maku ya ayyana aniyarsa ta takarar kujerar gwamnan Nasarawa

Mustapha Sule Lamido na hararo kujerar gwamnan Jigawa

A Jigawa, dan tsohon gwamnan jihar kuma jigon jam'iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido, na kokarin karbe ragamar mulkin jihar.

Mustapha Sule Lamido tuni ya siya fom na takarar gwamnan jihar Jigawa karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Dan Bafarawa, Sagir, ya zaburo takarar gwamnan Sokoto

Kwamishinan muhalli na jihar Sokoto, Sagir Bafarawa ya bayyana burinsa na takarar kujerar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar PDP.

Kwamishinan, wanda da ne ga tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya sanar da hakan a wani taro da yayi da shugabannin jam'iyyar PDP na jihar.

Ya ce, "Jam'iyya ta fi komai a siyasa, hakan yasa dole na yi taron nan da shugabannin jam'iyya domin ku saka min albarka.
"Duk da shugabannin jam'iyya sun aminta da burina, ina son tabbatar muku da cewa da izinin Allah zan yi nasara, zan dasa daga inda Gwamna Aminu Tambuwal ya tsaya."

Kara karanta wannan

Ba na shakkan Tinubu ko Osinbajo, duk zan kada su - Yahaya Bello

Dan Adamu Mu'azu ya shige jerin manema kujerar gwamnan jihar Bauchi

Dan tsohon gwamnan jhar Bauchi, Ahmadu Adamu Mu'azu, ya bayyana burinsa na takarar gwamnan jihar a shekarar 2023 a karkashin inuwar jam'iyya PDP.

Ahmed Ahmadu Adamu Mu'azu, wanda ke da suna iri daya da na mahaifinsa, ya siya fom din takara kuma ya fara tsara yanayin kamfen dinsa.

Pam Jonah Jang ya fito takarar dan majalisar wakilai a Filato

Pam Jonah Jang, dan tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, ya bi ayari, ya shiga neman takarar kujerar majalisar wakilai ta mazabar Jos ta kudu da Jos ta gabas a zaben 2023.

Kwamitin abokai ne suka siyasa masa fom karkashin jam'iyyar PDP kuma suka gabatar masa da shi.

A yayin gabatar masa da fom din wani biki da aka yi a otal din Tamarald da ke Jos, Dr Dagwom D Toang ya ce, "Mun tsamo shi ne saboda muna son wakilci nagari a mazabar mu a 2023."

Kara karanta wannan

Yan Najeriya zasu zabi APC a 2023 saboda gwamnati na ta yi namijin kokari, Shugaba Buhari

Dan El-Rufai, Bello, na hango kujerrar majalisar wakilai

Bello, dan gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya shiga tseren zama dan majalisar wakilai a zaben shekarar 2023.

A cikin kwanakin nan ne fostocin kamfen din Bello El-Rufai suka watsu a kafafen sada zumuntar zamani.

Idan za a tuna, an nada Bello babban hadimin Sanata Uba Sani a shekarar 2019.

Bayan bayyanar burin Bello, dan majalisar wakilai mai wakilcin mazabar Kaduna ta arewa, Honarabul Samaila Suleiman, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng