Shirin 2023: Osinbajo ya tara gwamnonin APC don shaida musu aniyarsa ta gaje Buhari
- A yau ne mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya tara gwamnonin APC domin su caccaka tsinke
- Ya shirya bikin buda baki, inda zai bayyana masu aniyarsa ta gaje shugaban kasa Buhari a zaben 2023
- Majiyoyi daga Villa sun bayyana cewa, gwamnoni sun hallara, musamman ma na yankin Arewacin Najeriya
Abuja - Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya tara mambobin kungiyar gwmanoni ta Progressive Governors Forum (PGF), a fadarsa ta Akinola Aguda House da ke fadar shugaban kasa a Villa, Abuja.
Wasu majiyoyi na kusa da ofishin mataimakin shugaban kasar sun nuna cewa Osinbajo zai yi amfani da wannan damar ne wajen jin shawarin gwamnonin kan kudirinsa na gaje kujerar shugaban kasa a zaben 2023.
Da misalin karfe 6:45 na yamma, gwamnonin da ba su gaza shida ba, da suka hada da Mallam Nasir El-Rufa’i (Kaduna) da Dapo Abiodun (Ogun) sun riga sun shiga harabar fadar ta Osinbajo.
Sauran Gwamnonin APC da aka ga suna shigowa kafin karfe 7 na yamma da aka shirya gudanar da taron su ne: Hope Uzodinma (Imo); Babajide Sanwo-Olu (Lagos) and Gboyega Oyetola (Osun).
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wata majiya ta shaida wa jaridar The Nation cewa, Oyetola na can kasa mai tsarki, Makkah don gudanar da aikin Umrah, lamarin da ya kai ga yada rade-radin cewa motar Gwamnan na iya shigowa dauke da mataimakinsa Benedict Alabi.
Taron wanda ya aka shirya don gwamnonin da aka gayyata kawai da wasu mataimakansu, bai bar kofar shiga ga ‘yan jarid a harabar gidan mataimakin shugaban kasa ba.
Wata majiya a fadar Villa ta shaida jaridar Punch cewa:
“Taron buda baki da VP ya shirya yanzu yake farawa. Tuni dai gwamnonin APC musamman na Arewa suka taru. Yanzu dai VP zai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa. Sannan zai bayyana hakan ga dukkan ‘yan Najeriya."
Zamu zabi kowace hanya da muke da ita wajen fitar da wanda zai gaji Buhari, Sanata Adamu
A wani labarin, jam'iyyar APC ta shirya amfani da kowane ɗaya ɗaga cikin hanyar kato bayan kato, Deleget, da Sulhu wajen fitar da ɗan takarar shugaɓan ƙasa a zaɓen 2023.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanya wa'adin 3 ga watan Yuni kowace jam'iyyar siyasa ta gabatar mata da ɗan takararta, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Da yake jawabi ga manema labaran gidan gwamnati jim kaɗan bayan ganawa da shugaba Buhari, shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce jam'iyya mai mulki ta shirya wa kowane ɗaya ɗaga cikin zabi uku.
Asali: Legit.ng