Da dumi-dumi: Matar gwamnan APC ta shiga jerin 'yan takarar sanata a jiharsu
- Matar gwamnan jihar Ondo ta fito ta bayyana aniyar tsayawa takarar sanata daga yankinsu a jihar ta Ondo
- Ta bayyana haka ne ga manema labarai, inda ta bayyana manufofin da take son cimmawa ida ta samu dama
- Ta bayyana haka ne jim kadan bayan da matar tsohon gwamnan jihar Anambra ta bayyana irin wannan aniya a yankinsu
Jihar Ondo - Wani rahoton Daily Trust ya bayyana cewa, matar gwamnan jihar Ondo, Mrs. Betty Anyanwu-Akeredolu, ta shiga tseren takarar Sanata a zaben 2023.
Da take yiwa manema labarai jawabi a Owerri, babban birnin jihar Imo, a ranar Juma’a, Uwargidan gwamnan Ondo ta ce tana da sha’awar wakiltar mazabar Imo ta Gabas saboda tana son kawo sauyi a yankin.
A halin yanzu dai Sanata Onyewuchi Francis Ezenwa na jam'iyyar PDP ne ke wakiltar gundumar a zauren majalisar dokoki ta kasa.
Misis Akeredolu, wacce ta yi magana da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) a garin Owerri, ta ce shiyyar Sanatan Owerri ta Yamma ta sha fama da gurbataccen wakilci a tsawon shekaru.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta ce gwamnatocin baya-bayan nan a jihar Imo sun yi watsi da shiyyar, inda ta bayyana cewa ta fito takara ne domin ciyar da yankin gaba.
Ta ce za ta iyawa da gogewar da ta samu a ciki da wajen kasar nan domin kawo ci gaba yankin.
Ta ce tana ci gaba da tuntubar jama'arta kuma idan aka zabe ta a matsayin Sanata, za ta karfafa al'ummar yankin.
Manufofin da take son cimmawa
Hakazalika, ta kuma bayyana irin manufofin da take da burin cimmawa matukar ta samu damar wakiltar yankin, kamar yadda New Telegraph ta tattaro.
A cewarta, za ta dauki matakai na taimaka wa manoman karkara da kayayyakin aikin gona na zamani, inganta ilmin yara mata, kawar da cutar da ke kashe yara da kuma uwa uba rashin aikin yi a cikin matasa.
Matan shugabanni a Najeriya na ci gaba da nuna sha'awar dalewa kujerun siyasa a zabe mai zuwa na 2023.
Matar Akeredolu ta shiga takarar ne bayan da Mrs Ebelechukwu Obiano, uwargidan tsohon gwamnan Anambra, ta sayi fom din tsayawa takarar majalisar dattawa a makon jiya.
A wani labarin, kotun daukaka kara reshen Enugu, a ranar Juma’a ta kori karar da ke neman a tsige Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi da mataimakinsa Kelechi Igwe daga ofis saboda sauya sheka zuwa wata jam’iyya.
'Yan siyasan biyu sun koma jam'iyyar APC ne daga jam’iyyar PDP a watan Nuwamban 2020, Premium Times ta ruwaito.
Bayan sauya shekar tasu, dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamna na 2019, Sonni Ogbuoji, da mataimakinsa, Justin Mbam, sun garzaya wata babbar kotun jihar Ebonyi suna neman ta kori gwamnan da mataimakinsa daga kujerunsu.
Asali: Legit.ng