PDP ta na fuskantar barazana a jihohin Kudu idan ta ba Atiku, Saraki ko Tambuwal takara

PDP ta na fuskantar barazana a jihohin Kudu idan ta ba Atiku, Saraki ko Tambuwal takara

  • Akwai yiwuwar jam’iyyar PDP ta tsaida ‘dan takarar shugaban kasan ta daga Arewacin Najeriya
  • Ba dole ba ne ‘Dan takarar da PDP za ta dauko ya iya galaba a kan jam’iyyar APC a yankin Arewa
  • Hakan zai iya jawo PDP ta rasa Delta, Oyo, Ribas, Abia, Enugu da kuma Benuwai a zaben gwamnoni

Abuja - Ko da har yanzu ba a tabbatar da matsayar kwamitin rabon mukamai da jam’iyyar PDP ya dauka ba, ana zargin za a bar kofar takarar 2023 ne a bude.

This Day ta ce matakin nan zai iya jawo tutar PDP ta fada hannun ‘dan siyasar Arewa. Amma hakan na da tasiri musamman a wasu jihohin da ke kudu.

Idan ‘dan takarar shugaban kasan PDP ya fito daga Arewa, zai taba kuri'un Oyo, Delta, Ribas, Abia, Enugu, Akwa Ibom, Benue da Kuros Riba a zaben gwamnoni.

Kara karanta wannan

Neman kujerar Shugaban kasa ya barka Atiku, Saraki da ‘Yan takarar PDP, kai ya rabu 3

Kungiyoyin kudu kamar PANDEF da Ohanaeze Ndigbo na yi wa PDP barazanar cewa mika tikiti ga mutumin Arewa kamar yadda aka yi a 2019, kuskure ne.

Matsalar da PDP za ta samu

Wannan mataki ba zai sa jam’iyyar hamayyar ta tashi da kuri’u masu yawa daga yankin Arewa ba. Akwai jihohin da duk abin da aka yi, PDP ba ta cin zabe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar ta na ganin har yanzu APC ta na da karfi a Arewa, inda nan kuri’u su ka fi yawa. Zai yi wahala ‘dan takarar da PDP za ta dauka ya doke APC a yankin.

Jam'iyyar PDP
'Yan PDP ana kamfe a Kano Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Wannan bincike da masana su ka yi ya nuna mutane a wadannan jihohi za su fusata da matakin da aka dauka, har jam’iyyar APC ta samu kafa gwamnati a 2023.

Binciken da jaridar ta yi ya haska cewa ba abin mamaki ba ne jam’iyyar APC ta lashe kuri’un Yobe da Borno, duk da cewa ‘dan kudu ne zai yi takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Gardamar yankin da za a ba takarar shugaban kasa a zaben 2023 ya kawo rigima a PDP

Barin Kwankwaso jam'iyyar PDP

Sauya-shekar Rabiu Kwankwanso zuwa NNPP zai iya ta kawowa jam’iyyar PDP babban cikas musamman a Kano. Samun kuri’u a Kano zai yi wa PDP wahala.

Tsohon gwamnan na Kano ya na cikin 'yan siyasa masu yawan mabiya musamman a Arewa.

Ana tunanin Adamawa kadai PDP za ta iya tsira da ita a Arewa. A halin yanzu PDP ta na rike da Bauchi, Benuwai, da kuma Taraba (inda PDP ba ta taba rasawa ba).

Asara a jihohin Kudancin Najeriya

Idan PDP tayi sake, jihohin da suke hannunta a bangaren Kudu maso kudu da kuma Kudu maso gabashin Najeriya za su koma ga APC da za ta kai takara yankin.

A zaben shugaban kasa, wadannan yankuna su na cikin mafi karantar kuri'u da kokarin fita zabe.

Fayose zai nemi takara a PDP

Ana haka ne sai aka ji cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose ya yi murabus daga kwamitin jam'iyyar PDP na kason kujerun siyasa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Zaben APC: Goyon bayan Buhari, sanin siyasa da abubuwa 4 da suka taimakawa Adamu

Tsohon gwamnan na jihar Ekiti ya dauki wannan mataki ne domin ya na da niyyar yin takara a 2023, bayan an ji shi ya na cewa ya na tare da Gwamna Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel