Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Wa Sojoji Hari, Sun Bankawa Motar Sojojin Wuta

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Wa Sojoji Hari, Sun Bankawa Motar Sojojin Wuta

  • Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton yan kungiyar IPOB ne sun kai wa sojoji da ke sintiri a cikin mota hari a Aba
  • Rahotanni sun bayyana cewa miyagun sun labe ne suka mamayi sojojin kuma daga bisani sun cinnawa motar sojojin wuta
  • Wata majiya daga hukumar tsaro ta tabbatar da afkuwar lamarin tana mai cewa ya faru ne misalin karfe 3 na dare

Aba, Jihar Abia - Wasu yan bindiga da ake zargin yan kungiyar masu neman kafa Biafara, IPOB, sun kai wa motar sintiri na sojoji hari a Aba, a Jihar Abia.

The Nation ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Juma'a a lokacin da sojojin ke aikin sintiri.

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Wa Sojoji Hari, Sun Bankawa Motar Sojojin Wuta
'Yan Bindiga Sun Kai Wa Sojoji Hari a Abia, Sun Bankawa Motar Sojojin Wuta. Hoto: The Nation.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu ta yi watsi da laifuka 8 cikin 15 da ake tuhumar Nnamdi Kanu da su

An gano cewa maharan sun labe ne sun kai wa sojojin harin kwantar bauna.

Lamarin ya faru ne a shahararren mahadar Tonimas da ke karamar hukumar Osisioma a babban hanyar Enugu-Aba-Port Harcourt, rahoton Vanguard.

Maharan sun kuma kona motar sintirin sojojin.

Amma, a yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ba sakamakon harin.

Majiya ta tsaro ta tabbatar da afkuwar harin da miyagun suka kai wa sojoji

Wata majiya daga hukumomin tsaro ta ce lamarin ya faru ne misalin karfe 3 na dare.

An tattaro bayanai cewa lamarin ya janyo tashin hankali a unguwar inda mazauna ke zaman dar-dar.

Harin Jirgin Ƙasa: Idan Sojojin Mu Sun Gaza, Na Rantse, Zan Ɗakko Sojojin Haya Daga Kasar Waje – El-Rufai

A bangarensa, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya lashi takobin yin hayar sojoji daga kasashen ketare don su taya yaki da ‘yan ta’adda bayan harin da suka kai wa jirgin kasa a Kaduna ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Yan ta’adda sun farmaki asibiti da kwalejin mata a jihar Borno

Ya kuma lissafo jihohi 4 na yankin arewa maso yamma, inda ya ce akwai yuwuwar su bi sahun shi. Jihohin sun hada da Zamfara, Kebbi, Katsina da Sokoto, The Punch ta ruwaito.

Ya ce zasu dauki wannan matakin ne matsawar gwamnatin tarayya bata dauki wani matakin a zo a gani ba a yankin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel