Yanzu-yanzu: Kotu ta yi watsi da laifuka 8 cikin 15 da ake tuhumar Nnamdi Kanu da su

Yanzu-yanzu: Kotu ta yi watsi da laifuka 8 cikin 15 da ake tuhumar Nnamdi Kanu da su

  • Kotu ta cigaba da zamanta yau kan shari'ar shugaban kungiyar Biyafara IPOB, Nnamdi Kanu
  • Lauyoyin Nnamdi Kanu sun bukaci kotun ta bada belinsa kuma sun yi alkawarin ba zai sake guduwa ba
  • Alkalin kotun duk da amincewa da wasu bukatun lauyoyin ta dage zaman zuwa wata rana kan maganar belin

Maitama, Abuja - Babbar kotun tarayya dake Abuja ta yi watsi da laifuka takwas cikin goma sha biyar da gwamnatin tarayya ke tuhumar Nnamdi Kanu, da su.

Gwamnatin tarayya da dauko Nnamdi Kanu daga kasar Kenya inda ya gudu kuma ya makashi a kotu kan zargin aikata ayyukan ta'addanci.

Alkalin kotun, Binta Nyako, a zaman ranar Juma'a ta yi waje da laifuka takwas da gwamnati ke zargin Kanu ya aikata, rahoton ChannelsTV.

Kara karanta wannan

Zambar Daukan Aikin Immigration: Kotu Ta wanke Abba Moro, ta kama Sakatariya da laifi

Tace sun hada da na 6,7,8,9,10,11,12 da 14 saboda babu hujjar dake nuna cewa wanda ake zargi ya aikata laifukan.

Amma ta ce akwai alamun gaskiya cikin laifi na 1,2,3,4,5,13, da 15 kuma a kai za'a cigaba da gurfanar da Nnamdi Kanu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yanzu-yanzu: Kotu ta yi watsi da laifuka 8 cikin 15 da ake tuhumar Nnamdi Kanu da su
Yanzu-yanzu: Kotu ta yi watsi da laifuka 8 cikin 15 da ake tuhumar Nnamdi Kanu da su
Asali: Getty Images

Kotun tace daukoshi da akayi daga wata kasa ya gudu ya halatta saboda tuni an alanta nemansa ruwa a jallo.

Kotun ta dage zama.

Kotu za ta yi shari'ar sirri ga masu daukar nauyin Boko Haram da Nnamdi Kanu

Babban alkalin babbar kotun tarayya, Mai shari’a John Tsoho, ya fitar da wata sabuwar alkibla a batu shari’ar ta’addanci da ke gabanta, Daily Trust ta rahoto.

A halin yanzu dai shari’ar shugaban 'yan awaren Biafra, Nnamdi Kanu, da 'yan canjin da ake tuhumarsu da laifin daukar nauyin ayyukan ta’addanci suna gaban kotun.

Mai shari’a Tsoho ya ce sabuwar alkiblar shari'ar ita ce ta yin amfani da ikonsa na tsarin mulki kamar yadda yake a sashe na 254 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999.

Asali: Legit.ng

Online view pixel