Gonar kudi: Yadda matashi ya sayar da hoton tsaleliyar budurwa N600k a duniyar crypto

Gonar kudi: Yadda matashi ya sayar da hoton tsaleliyar budurwa N600k a duniyar crypto

  • Wani hazikin mai daukar hoto a Najeriya, Adisa Olashile, ya mayar da hoton wata tsaleliyar budurwa NFT, inda ya sayar da shi kan 0.35 Eth (N675,748.546)
  • Mutumin da ya gode wa dandalin Foundation, inda ya sayar da hoton, ya kuma bayyana cewa har yanzu yana da sauran hotuna biyar na NFT
  • 'Yan Najeriya da dama sun yi dafifi a sashen sharhi domin taya shi murna, yayin da wasu suka nemi ya koya musu fasahar NFT

Wani hazikin matashin madaukin hotuna a Najeriya, Adisa Olashile, ya yi amfani da karfin fasahar blockchain ta hada-hadar kudaden intanet wajen cika aljihunsa da kudi.

Wannan na zuwa ne kwanaki bayan da ya sayar da hotunan wani tsohon makadi a kafar NFT ta OpenSea kan kudi sama da miliyan daya. Sannan ya yi alkawarin bai wa tsohon 50% na abin da ya samu.

Kara karanta wannan

Masu fasa bututu sun taso Najeriya a gaba, ana asarar Naira Biliyan 600 a kowace rana

Kudi na duniyar crypto, wani ya sayar da hoton budurwa
Gonar kudi: Yadda matashi ya sayar da hoton tsaleliyar budurwa N600k a duniyar crypto | Hoto: @adisaolashile
Asali: Twitter

Yadda ya siyar da hoton

A cikin wani rubutu a ranar Laraba, 6 ga Afrilu, hazikin matashin ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa ya siyar da hoton wata budurwa a matsayin Non-Fungible Token (NFT) akan Foundation, wata kafar musayar NFT.

An siya hoton ne ta tsarin NFT, @a5htr, akan 0.35 na Ethereum (ETH). Adisa ya bayyana cewa har yanzu yana da kwafi guda biyar da ya rage na sayarwa na hotunan.

A lokacin rubuta wannan rahoto, farashin 0.35 ETH/USDT a kasuwar kudin intanet ta Binance ya kai $1148.49 (N675,748.546) yayin da farashin ETH 1 ke kan $3281.42 (N1,930,721.9).

Ya kamata ku lura cewa farashin kudaden intanet basu da tabbas, komai zai iya faruwa idan aka samu sauyi a kasuwa.

A lokacin rubuta wannan rahoto, rubutun da ya yi a Twitter ya tattara dubban-dubatar martani tare da dangwale sama da 400.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya yi sabon nadi, ya nada sabon ministan muhalli

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

@ClitonClit2 ya ce:

"Dan uwa ina DM dinka Ina bukatan taimakon ka akan NFT."

@Blackbody ya ce:

"Waw! Wani nasaran kuma, ina taya murna."

@teexels ya ce:

"Ina taya ka murna Adisa! Na san irin wannan! Kuma za a sayar da kai nan ba da dadewa ba!!! A halin yanzu ina da gwanjon wani kadan da ya rage! LFG."

@AnnaRostphoto ya ce:

"Na taya ka murna! Hoto mai kyau sosai!"

@tatchero ya ce:

"Kwarai kuwa! Ina taya ka murna dan dangi.!"

@Abiodunsax ya ce:

"Ina taya ka matukar murna dan uwa! Fatan karin nasara."

Abin da ka raina: Yadda matashi ya dauki hoton makadi, ya sayar N1.2m a duniyar Crypto

A wani labarin, wani matashi madaukin hotuna a Najeriya, Adisa Olashile, ya nuna daya daga cikin damammaki masu yawa na duniyar kudaden intanet wato blockchain da cryptocurrency ta kunsa.

Kara karanta wannan

Abin da ka raina: Yadda matashi ya dauki hoton makadi, ya sayar N1.2m a duniyar Crypto

A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a, 1 ga Afrilu, Adisa ya ce ya dauki hotunan wani tsohon makadi wanda ya saba gani a hanyarsa ta zuwa hidimar ci gaban al’umma ta CDS ta NYSC.

A ranar Asabar, 2 ga Afrilu, madaukin hotunan ya hau Twitter inda ya bayyana cewa ya sauya hotunan tsohon makadin zuwa Non-Fungible Token (NFT) a kasuwar OpenSea kuma ya sayar da su akan 0.3 Ethereum (Eth) kowanne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel