Tsohon Gwamna ya maka Ministan shari’a gaban Alkali, ya na neman a biya shi N1.5bn

Tsohon Gwamna ya maka Ministan shari’a gaban Alkali, ya na neman a biya shi N1.5bn

  • Victor Obong Attah wanda ya taba yin gwamna a jihar Akwa Ibom ya shigar da kara a kotun tarayya
  • Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom ya na karar Ministan shari’a na tarayya, Abubakar Malami SAN
  • Attah ya bukaci AGF ya biya sa diyyar N1.5bn saboda ya ci masa zarafi da zargin da ya jefa masa

Abuja - Kamar yadda Punch ta fitar da rahoto a ranar Laraba, Victor Attah ya na tuhumar babban lauyan na gwamnatin kasa da neman mata masa suna.

Attah ya shigar da wannan kara ne gaban Alkalin babban kotun tarayya da ke zama a Abuja, Emeka Nwite ta hannun lauyan nan, Dr. Reuben Atabo.

Dr. Reuben Atabo SAN ya fadawa kotu cewa a shekarar 2016, Abubakar Malami SAN ya ambaci Attah a cikin tsofaffin gwamnonin da ake zargi da laifi.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamnan Anambra ya ba Buhari shawarar abin da ya kamata ayi wa Nnamdi Kanu

Ministan ya shaidawa Duniya cewa kwamitin nan na National Prosecution Coordination, ya na tuhumar tsohon gwamnan Akwa Ibom da rashin gaskiya.

A korafin da ya gabatarwa Alkali, babban lauyan ya bayyana cewa ikirarin da Malami ya yi, wanda ya shiga gidajen yada labarai, ya jefa Attah a matsala.

Dr. Atabo ya ce a dalilin wannan ne ‘yan sandan kasar Birtaniya suka makawa Attah takunkumi, su ka sa shi a sahun tsofaffin gwamnoni marasa gaskiya.

Tsohon Gwamnan PDP
Victor Attah Hoto: Legit.ng Daga: Samuel Olubiyo
Asali: Original

Jawabin Victor Attah

“Na bar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2007, kuma zargin da yake kai na da gwamnati na shi ne karkatar da kudin da aka samu wajen saida hannun jarin jihar Akwa Ibom da ke kamfanin Econet.”
“Kuma na wanke kai na daga wadannan zargi. Daga Mayun 2007, babu wani sabon zargi da aka yi mani na karkatar da dukiyar Akwa Ibom, satar kudi, cin amanar ofis ko wani rashin gaskiya.”

Kara karanta wannan

2023: Wike ya jagoranci gwamnonin PDP zuwa wajen Janar Babangida da Abdussalami

"Abin da wanda ake zargi ya aikata, ya jawo SCD da ‘yan sandan birtaniya sun sa sunana a cikin wadanda ake sa wa ido, ana jiran idan na zo Ingila, ayi ram da ni domin a bincike ni.”

- Victor Attah

Na yi asarar kwangiloli da mutunci

“Tun lokacin ban iya zuwa kasar Birtaniya domin yin harkokina ba, na yi asarar kwangiloli da yawa.”

Tun daga lokacin da Malami ya yi wannan magana, Attah ya ce aka taso shi gaba, aka zubar masa da mutunci, har ana cewa bai dace ya rike wani mukami ba.

Hakan ta sa ya nemi AGF ya janye kalaman, ya rubutawa SCD takarda ya wanke shi, kuma ya bada hakuri, sannan ya na neman N1.5bn saboda ci masa zarafi.

An rahoto a Nairaland cewa Malami ya fadawa kotu cewa ba su da hurumin da za su saurari karar.

Ayade ya sha a kotu

Kara karanta wannan

Sau uku Ubangiji na kirana, ya ce Atiku ne zai gaji Buhari a 2023, inji Dino Malaye

An ji cewa Gwamnan Kuros Riba ya fadi abin da zai yi muddin aka tsige shi a kotu saboda barin PDP. Ben Ayade ya ce ya yarda da kotu, dole zai rungumi kaddara.

Jim kadan sai aka ji cewa Alkali bai sauke shi daga kan mulki ba duk da ya sauya-sheka. Mai shari'a Taiwo Taiwo ya ce kotunsa bai da hurumin tsige gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel