Bayan Watanni 10, Har Yanzu Ɗaliban Yauri Mata 11 Suna Hannun Ƴan Ta'adda

Bayan Watanni 10, Har Yanzu Ɗaliban Yauri Mata 11 Suna Hannun Ƴan Ta'adda

  • Nan da kwana 10, dalibai 11 mata na kwalejin gwamnatin tarayya da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi, za su cika watanni 10 a hannun ‘yan bindiga
  • Fitaccen dan bindigar nan, Dogo Gide ne ke da alhakin sace daliban yayin da suka kai farmaki a ranar 17 ga watan Yunin da ta gabata
  • Sakamakon harin, sun yi garkuwa da dalibai da yawa da malamai 5, bayan nan an biya kudin fansa kashi-kashi amma har yanzu guda 11 suna hannunsu

Kebbi - Sakamakon farmakin da fitaccen dan bindiga, Dogo Gide da yaransa suka kai Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi, sun sace dalibai da malamai sannan sun saki wasu, yanzu haka 11 daga cikin dalibai mata zasu cika watanni 10 a hannunsu.

Kara karanta wannan

Sabon hari: Bayan ziyarar IGP Kaduna, 'yan bindiga sun bi gida-gida sun sace mutane 22

A ranar 17 ga watan Yunin shekarar da ta gabata suka kai farmakin FGGC Birnin Yauri inda suka yi garkuwa da dalibai da yawa da malamai biyar.

Bayan Watanni 10, Har Yanzu Ɗaliban Yauri Mata 11 Suna Hannun Ƴan Ta'adda
Bayan Wata 10, Har Yanzu Akwai Sauran Ɗaliban Yauri Mata 11 a Hannun Ƴan Ta'adda. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Duk da an biya su kudaden fansa a karo daban-daban, amma har yanzu dalibai mata 11 suna hannunsu.

A ranar 21 ga watan Fabrairu, Daily Trust ta ruwaito yadda ‘yan ta’addan suka auri fiye da dalibai mata 13 da ke hannunsu, kuma yanzu haka wasu suna da ciki.

Kafin wannan harin akwai wasu hare-haren da suka kai

Daily Trust ta tunatar da yadda ‘yan bindigan suka dinga kai hare-hare makarantu akalla 10 da ke Jihar Zamfara, Kaduna, Neja da Kebbi a shekarar da ta gabata.

A watan Disamban 2020 ne wata kungiyar ‘yan ta’adda wacce wani Auwal Daudawa ke jagoranta ta kai farmaki makarantar sakandaren kimiyya da ke Kankara a Jihar Katsina inda ta sace fiye da dalibai 200.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun bindige dan kwamishinan tsaron Zamfara lokacin buda baki

Bai wuci kwana 20 ba ne tazarar farmakin da suka kai FGC Yauri da kuma wacce suka kai makarantar Islamiyyar Salihu Tanko da ke Tegina a Jihar Neja inda suka sace dalibai da dama. Hakan ya yi matukar tayar da hankulan jama’a.

Yanzu haka wasu daliban suna da ciki

Bayan satar ne jami’an tsaro suka yi gaggawar amso wasu daga cikin daliban yayin da sai da aka tattauna da su sannan suka sako su.

Ana zargin Gide yana da alaka da kungiyar jihadi ta Jama’atu Ansarul Muslimina Fi Bilad as-Sudan, wacce aka fi sani da Ansaru, kuma yayin tattaunawa da shi ya yi ikirarin mayar da dalibai maza ‘yan bindiga yayin da ya ce zai aurar da matan.

Wadanda suka yi kokarin ceto daliban da ‘yan ta’addan suka sace sun sanar da Daily Trust cewa dan ta’addan ya zartar da kudirinsa kuma akalla ya aurar da dalibai fiye da 13.

Kara karanta wannan

Sifetan dan sanda ya sheka lahira yana tsaka da 'kece raini' da bazawara a otal

Ana zargin an mika daliban ne ga ‘yan ta’addan ISWAP, kamar yadda iyayen daya daga cikin dalibai mata wadanda suka bukaci a sakaya sunansu suka shaida.

Sannan an samu bayani akan dalibai matan da aka aurar da su ga wasu mazauna kauyen da Gide ya ke juyawa da ke Birnin Gwari.

Akwai dalibar da mahaifiyarta ta biya kudin fansarta N2m suka amshe suka ki sakinta

Duk da dai an biya su kudin fansa, har yanzu basu saki wasu daga cikin daliban ba, kuma Gide ya bukaci a saki wasu yaransa biyu da ke hannun hukuma a matsayin sharadin zai sanya ya saki daliban da ke hannunsa.

Sai dai dan aiken da ke kai sako daga iyayen yaran zuwa ‘yan ta’addan ya ce an saki daya daga cikin daliban a tsakiyar watan Janairu inda yanzu suka koma 12 a hannun ‘yan bindigan. Akwai wasu ukun da aka saki wadanda suka dawo da ciki.

Kara karanta wannan

'Yan Ta'adda Sun Ji Ba Daɗi Yayin Da Sojoji Suka Kashe Fiye Da 85 a Kaduna, Zamfara Da Borno

Daily Trust ta gano cewa yanzu haka akwai dalibai mata 11 a hannun ‘yan bindigan. Kuma Gide ya bukaci Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar da gwamnati zata biya, amma har yanzu shiru.

An samu bayani akan yadda iyayen daya daga cikin daliban ta biya Naira miliyan 2 ga ‘yan bindigan amma har yanzu basu sako diyarta ba kuma yanzu sun dena daga wayarta.

'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun halaka jama'a masu yawa a sabon harin da suka kai Benue

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel