Musulmai sun caccaki gwamnan Ondo kan shirin dankawa Kiristoci wasu makarantu

Musulmai sun caccaki gwamnan Ondo kan shirin dankawa Kiristoci wasu makarantu

  • Limamai, Alfa-Alfa, da manyan malaman addinin Musulunci a jihar Ondo sun ce zasu yi fito-na-fito da Gwamnan jihar
  • Shugabannin Musulman sun ce Gwamnan ya kammala shirin mayar da makarantun gwamnati na Mission
  • Malaman sun ce idan gwamnan bai dakata daga abinda yake shirin yi ba zasu shiga kotu

Akure - Al'ummar Musulmin jihar Ondo sun bayyana rashin amincewarsu ga shirin da Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar ke shirin yi na dankawa Kiristoci makarantun gwamnati.

Musulman sun ce wannan ba karamin koma baya zai janyowa ilimi ba a jihar.

Sun lashi takobin cewa idan gwamnan yaki sauya ra'ayinsa, zasu kai shi kotu.

Musulman sun ce mikawa Kiristoci makarantar zai sababba korar yaransu daga makarantu ko kuma a rika musguna musu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari Masallaci lokacin bude baki, sun kashe mutum 3, sun yi awon gaba da wasu

Musulmai sun caccaki gwamnan Ondo kan shirin dankawa Kiristoci wasu makarantu
Musulmai sun caccaki gwamnan Ondo kan shirin dankawa Kiristoci wasu makarantu Hoto: Kwara State/Dalibai
Asali: Twitter

Shugaban Limamai da Malaman jihar, Sheikh Ahmad Aladesawe, a hira da manema labarai ya ce ba zasu yarda ba, rahoton TheNation.

Sheikh Ahmad wanda ya samu wakilcin Sakataren kungiyar, Alhaji Abdulrasheed Akerele, yace gwamnatin na kokarin karfafa addinin Kirista ta hanyar damka musu makarantun gwamnati.

Aladesawe yace:

"Ya na son mikawa wasu daidaikun mutane dukiyar al'umma da sunan mikawa kungiyoyin addini. Wannan cuta ne kuma koma baya."
"Shin su yan mission din da ake shirin dankawa makarantun zasu biya kudi ne da darajar Dala 2 zuwa Naira 1.?"
"Muna kira ga cewa ikirarin cewa makarantun mallakin wasu kungiyoyin addini ne farfaganda ne kawai."
"Kawai so ake a mayar da makarantu hannun Coci da masu da'awar Kirista. So ake a hana dalibai Musulmai samun ingantaccen Ilimi."

Kara karanta wannan

Ramadana: Yin azumi na karawa mutum karfi da lafiyar jiki – In ji kwararriyar likita

Ina tare da dalibai mata Musulmai, babu wanda ya isa ya hanasu sanya Hijabi: Gwamnan Kwara

A wani labarin kuwa, Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya bayyana cewa ko shakka babu yana tare da dalibai mata Musulmai kan lamarin sanya Hijabi cikin makarantun jihar.

Yace wannan ita ce matsayarsa saboda shari'o'in da kotu ta yanke kan lamarin da kuma kasancewar Kwara jiha mai daidaito tsakanin addinai kuma jihar da tafi kama da kudu wajen adadin masu addinai mabananta.

Abdulrazaq yace gwamnatinsa kawai doka da gaskiya take bi da kuma nuna adalci tsakanin kowa, sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakaye, ya bayyana

Asali: Legit.ng

Online view pixel