Sheikh Bala Lau ya gina katafariyar makaranta a Jimeta (hotuna)
A ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, an kaddamar da katafaren makarantar haddan Al-Qur’ani mai girma wanda shugaban kungiyar Izala Ash-Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ya gina a garin Yola, babban jihar Adamwa. An kuma sanya ma makarantar suna 'Na'bi Academy'.
An kera makarantar ne irin ginin zamani, sannan kuma an kaddamar da ita ne domin haddan littafi mai tsarki ga yara yan shekaru uku zuwa shekaru shida, za’a kuma basu haddan Al-Qur’ani cikin shekaru uku da yardarm Allah.
An kuma tanaji dukkan wani abu da dalibai zasu bukata, kama daga abinci zuwa masu yi musu hidima, tare da kwararrun malamai da za su horar da su.
Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jibwis Yola ta Arewa Sheikh Ali Mamman, shi ya jagoranci kaddamar da karatun, tare da malaman makarantar.
Har ila yau shugaban Makarantar, Malam Aliyu Abubakar ya shaida mana cewa yanzu haka ana daukan dalibai, inda ake sayan takardan cikewa (Form) domin shiga makarantar.
KU KARANTA KUMA: Buratai ya rubuta wasika na musamman don ba da tabbaci ga sojoji
Shima Ustaz Jabir, sakataren kwamitin kula da makarantar, a bayanan sa yace cikin shekaru uku ne ake so yaran su haddace Al-Qur'ani mai girma, inda aka shirya basu haddar izu ishirin ko wace shekara insha Allah.
Ga karin hotunan makarantar:
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng