Ganin saukar bakon jirgin sama: Jami'an tsaro sun bincike dajin Ogbomoso ciki da waje
- Jama'a mazauna kusa da yankunan dajikan Ogbomoso sun bayyana cewa wani bakon jirgin sama na sauka a tsauni inda yake kai wa miyagu kayayyaki
- Tuni tawagar jami'an hadin guiwa da suka hada da 'yan sanda, sojoji da NSCDC suka bincike dajikan domin bankado miyagun
- Sahihin labari daga jami'an tsaron ya bayyana cewa karya ne babu wani dan ta'adda a cikin dajikan, labaran kanzon kurege ne kawai
Ogbomoso, Oyo - Rundunar ‘yan sandan Najeriya, rundunar ‘yan sandan Amotekun da ‘Operation Burst’ wacce rundunar hadin guiwa ce ta jami’an tsaro da ta kunshi sojoji da jami’an tsaron farin kaya da na Civil Defence, sun cike dazuzzukan wasu kananan hukumomi uku a garin Ogbomoso na jihar Oyo, domin neman ‘yan ta'addan da ke taruwa a wurin.
Punch ta ruwaito cewa, an yi ta rade-radin cewa an ga wani jirgi mai saukar ungulu yana sauka a kan wani tudu a daya daga cikin dazuzzukan yana bayar da makamai da harsasai ga ‘yan fashin da ke taruwa a wurin.
Amma kuma, bayan shafe sa’o’i da dama ana zagaya dazuzzukan ta hanyar amfani da ababen hawa, babura da kuma ‘yan sintiri na kafa da jami’an tsaro suka yi, an tattaro cewa ba a samu wani mai laifi ko ‘yan ta’adda a cikin dajin ba.
Shugaban kungiyar matasan yankin Ogbomoso, Rabaren Peter Olaleye, a lokacin da yake zantawa da manema labarai ta wayar tarho a ranar Laraba, ya ce shi da wasu ’yan kungiyar matasan sun jagoranci jami’an tsaro zuwa wuraren da wasu mazauna yankin suka ce ‘yan ta’adda na taruwa amma ba su samu kowa a wurin ba.
Olaleye ya ce, “Jami’an tsaro sun yi ta duba dazuzzuka a Ogbomoso domin neman ‘yan fashin da wasu ke ikirarin suna taruwa a wurin.
“Dazukan da ke kan iyaka da kananan hukumomi uku na Ogbomoso ta Kudu, Surulere da Ogo-Oluwa, a Odanbon/Ayegun Yemetu, ana rade-radin cewa akwai ‘yan fashi da dama, amma bayan da jami’an tsaro da dama suka zagaya dajin kwana biyu yanzu, babu wani abu da ya faru.
“A yau, rundunar hadin guiwar jami’an tsaro da suka hada da Operation Burst, Amotekun corps, ‘yan sanda da kuma tawagar ‘yan sanda muka duba dazuzzukan.
“Mun dawo daga binciken da yammacin nan, kuma ba a samu ‘yan fashi a ko’ina a cikin dajin ba.
“Akwai rade-radin cewa an ga wani jirgi mai saukar ungulu yana daukar makamai da alburusai ga wasu ‘yan bindiga da ke taruwa a kan tudu da ke cikin dajin kuma mun gayyaci jami’an tsaro. Mun yi farin ciki da gaggawar zuwansu. Muna yaba musu.”
Kwamandan Operation Burst a jihar Oyo, Kanal Olayinka Olayanju (mai ritaya), da aka tuntube shi ya tabbatar wa Punch faruwar hakan.
Ya ce, “Mu da Operation Burst mun fara bincike dazuzzuka a kananan hukumomin Ogo Oluwa da Surulere ranar Talata. Mun ci gaba a yau kuma ba mu samo komai ba.
“Wannan karya ce domin idan gaskiya ne hatta mutanen kauye za su sami shaidar daukar hoto na jirgin helikwafta da suke ikirarin ya kan zo wurin.
“Mun duba ko’ina kuma mun gamsu da abin da muka yi. Ba a samu wani dan fashi a ko'ina ba. Jita-jita ce kawai, kuma ina kira ga jama’armu da su yi daina yada wannan jita-jita.”
Asali: Legit.ng