Nisan kwana: Bidiyon busasshen tsohon da mutuwa ta mance dashi ya girgiza intanet

Nisan kwana: Bidiyon busasshen tsohon da mutuwa ta mance dashi ya girgiza intanet

  • Wani tsoho ya zama abin magana a intanet bayan da faifan bidiyonsa ya yadu a dandalin sada zumunta na TikTok
  • Mutumin da aka bayyana sunansa da Luang Pho Yai ya haifar da cece-kuce a yanar gizo yayin da wasu da dama suka yi kokarin tantance ainihin shekarunsa
  • Jikarsa da ta dauki bidiyoyinsa kuma ta saka su a TikTok ta sanya kudi ga wata tambaya ta musamman masu amfani da kafar ta TikTok

Sha’awar matasa da yawa ne su yi rayuwa mai tsawo, amma faifan bidiyo wani tsoho ya sa mutane da yawa sun sake tunani game da tsufa.

Tsohon mai suna Luang Pho Yai ya yi fice a dandalin sada zumunta na TikTok bayan da jikarsa ta fara yada bidiyonsa a kusan Nuwamba 2021, in ji Snopes.

Yadda tsoho ya ba da mamaki a Intanet
Nisan kwana: Bidiyon busasshen tsohon da mutuwa ta mance dashi ya girgiza intanet | Hoto: TikTok/@auyary13
Asali: UGC

Sakamakon ganin jemammiyar fatarsa da kwarangwal din jikinsa da ake iya gani, jama'a yanar gizo sun yi kokarin gano shekarunsa tare da yin ba'a game da yadda ya kasance a lokacin haihuwar Sarauniya Ingila Elizabeth da kuma lokutan Littafi Mai Tsarki.

Kara karanta wannan

Mubarak Bala: Martanin 'yan Najeriya kan hukuncin shekaru 24 da kotu ta yanke wa mulhidi

Jikar Luang ya bayyana ainihin shekarunsa

Jikarsa mai suna @Auyary13 ta bayyana cewa kakan nata yana da shekara 109 ne a duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai ba ta fayyace ko kamannin sa ya sauya ne sakamakon yin ibadar Sokushinbutsu - kalmar da ke nufin kekashe kai, wata al'adar sufaye na kasar Japan wanda aka ruwaito ya fara faruwa tsakanin 1081 zuwa 1903.

Yadda jikarsa ke ta dora faifan bidiyon nasa a TikTok ya samu karbuwa, inda miliyoyin mutane ke kallo kana ta samu mabiya da yawa a dandalin.

Kalli bidiyon:

Martanin 'yan soshiyal midiya

@StellaNnanna:

"Hian, wannan yayi yawa, ina nufin tana da ban tsoro."

@Lilcentasuquo1:

"Dari da tara kacal amma ta zama kamar haka? Ina tsammanin tana rashin lafiya sosai ba kawai tsufa bane."

@RichieB78550327:

"Abin tsoro.....amma bana addu'ar kaiwa kamar ta ooh.

Kara karanta wannan

Hotunan jaruma Nafisa Abdullahi yayin da ta je Umra, ta bayyana muhimmin abinda ta roki Allah

"Tana shan wahala tana wahala 'ya'yanta ma."

@purechocky:

"Na tabbata wadannan su ne mutanen zamanin da da suke bushewa da rana."

@lovina61144088

"A'a kam! Na ki irin wannan tsufar ga kaina.

Dan shekara 21 nake son aure: Yar shekara 70 da bata taba aure ba, bata taba sanin namiji ba

A wani labarin, wata mata yar shekara 70 mai suna Genevieve wacce bata taba aure ba ko saurayi ko sanin namjiji ba ta bayyana irin namijin da take so. Genevieve na fama da nakasar kafa wanda ke hanata tafiya.

A hirar da tayi da Afrimax, matar ta bayyana cewa ba haka aka haifeta ba a shekarar 1952. Amma daga baya iyayenta suka gani bata iya tafiya sai da rarrafe.

Ana kyautata zaton cewa Genevieve ta kamu da cutar ne lokacin tana yarinya wanda ya nakasa kafafunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.