Yan ta’adda sun farmaki asibiti da kwalejin mata a jihar Borno
- Yan ta'addan ISWAP sun kai hari yankin Damboa da ke jihar Borno a daren ranar Laraba, 6 ga watan Afrilu, yayin da ake tsaka da azumin watan Ramadana
- A yayin harin, tsagerun yan ta'addan sun kona wata cibiyar kiwon lafiya da kuma wasu bangarori na garin da kwalejin fasaha ta mata da ke yankin
- Maharan sun samu shiga yankin Damboa ne da kafa bayan sun ajiye baburansu a bayan wani babban rami da aka tona a kewayen garin
Borno - Sahara Reporters ta rahoto cewa wasu yan ta’adda da ake zargin mambobin kungiyar ISWAP ne sun kai farmaki garin Damboa da ke jihar Borno.
Wata majiya ta tsaro, wacce ta tabbatar da harin, ta ce yan ta’addan sun farmaki garin ne da misalin karfe 1:00 na tsakar daren ranar Laraba, 6 ga watan Afrilu, rahoton jaridar Punch.
Majiyar ta ce:
“Sun ajiye baburansu a bayan ramin da aka tona a kewayen garin sannan suka shiga da kafarsu."
Ya yi bayanin cewa sun kona wani bangare na cibiyar kiwon lafiya baya ga wasu bangarori na garin da kwalejin fasaha ta mata da ke Damboa.
Wani dan kungiyar yan sa kai ta CJTF ya kuma bayyana cewa wasu mambobinsu biyu sun jikkata sakamakon harbin bindiga.
'Yan bindiga sun shiga tasku: ‘Yan sanda suka fara sintiri ta sama a hanyar Abuja-Kaduna
A wani labarin, rundunar sintiri ta sama ta rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fara aikin sintiri da sa ido a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Matakin dai ci gaba ne da bin umarnin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba na cewa jami’an 'yan sandan Najeriya za su fara tsare hanyar.
IGP da ya ziyarci yankin a karshen makon da ya gabata ya yi wa ‘yan Najeriya alkawarin cewa ‘yan sanda za su tabbatar da tsaro a hanyar tare da tabbatar da tsaro ga duk masu ababen hawa da fasinjojin da ke bin hanyar.
Asali: Legit.ng