Yan bindiga sun kashe babban ɗan kasuwa a Katsina, sun sace ɗiyarsa da wasu mutum 7

Yan bindiga sun kashe babban ɗan kasuwa a Katsina, sun sace ɗiyarsa da wasu mutum 7

  • Wasu yan bindiga sun yi ajalin wani fitaccen ɗan kasuwa mai tausayin Talakawa a yankin Kankara ta jihar Katsina
  • Wani mazaunin yankin da abun ya faru ya ce maharan sun shiga kai tsaye gidan Alhaji Auta, suka fito da shi waje kuma suka kashe shi
  • Kakakin yan sandan Katsina, Gambo Isa, ya ce zai bincika, amma bayanai sun ce maharan sun sace wasu mutane

Katsina - A ranar Talatan nan, wasu yan bindiga suka kashe Sale Auta, shahararren ɗan kasuwa a ƙaramar hukumar Ƙanƙara, jihar Katsina, a harin dare da suka kai ƙauyen Daudau.

Yayin harin yan bindigan, wanda ake kyautata zaton yan ta'adda ne, sun yi garkuwa da ɗiyar mutumin, Aisha, da wasu mutane, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin Ƙasan Kaduna: Idan Sojojin Mu Sun Gaza, Na Rantse, Zan Ɗakko Sojojin Haya Daga Kasar Waje – El-Rufai

Yan ta'adda sun kashe ɗan kasuwa a Katsina.
Yan bindiga sun kashe babban ɗan kasuwa a Katsina, sun sace ɗiyarsa da wasu mutum 7 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Auta, Babban ɗan kasuwa kuma mutum mai tausayi da yi wa talakawa kyauta, ana tsammanin ya fi kowa dukiya a garin.

Wani mazaunin Kankara, Magaji Basiru, ya ce yan ta'addan sun zo a kan Babura, suka fito da shi waje, daga bisani kuma suka kashe shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Karfe 9:00 na dare ta ɗan wuce lokacin da na samu labarin harin. Alhaji Sule Auta na gida tare da wasu abokanansa yayin da yan bindiga suka shiga gidan suƙa ɗakko shi."

Basiru ya bayyana cewa mutanen dake zaune a garin suna zaton harin shiryayye ne da aka shirya domin mutumin kaɗai.

"Eh ina Kankara lokacin da yan bindiga suka kai hari kauyen, amma na samu labari yau Laraba cewa bayan Aisha, maharan sun yi garkuwa da wasu mutum 7, wasu sun ce 10."

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari kauyuka huɗu da tsakar rana a Zamfara, rayuka sun salwanta

Kakakin yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa, ya shaida wa wakilin jaridar cewa zai bincika kafin daga bisani ya dawo ya masa bayani, amma har yanzun shiru.

Jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin arewa maso yammacin ƙasar nan dake fama da rikicin yan bindiga, waɗan da ke kaddamar da hari kan ƙauyuka da matafiya.

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta zaɓi ranar zaben fidda ɗan takarar da zai gaji shugaba Buhari a zaɓen 2023

Jam'iyya mai mulki Najeriya ta sanya ranar da zata gudanar da zaɓen fitar da ɗan takararta na shugaban ƙasa a 2023.

Haka nan APC ta sanya ranar zaɓen fitar da yan takarar gwamna a jihohi 36, da yan majalisun dokoki da na tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262