Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kafa Sabbin Jami'o'i 12 a Yayin Da ASUU Ke Yajin Aiki
- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da kafa sabbin jami'oi 12 masu zaman kansu a jihohin kasar daban-daban
- An amince da wannan batun ne yayin taron FEC da aka gudanar a ranar Lahadi duk da cewa kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, tana yajin aiki
- Gwamnatin ta ce tsaffin jami'o'in da ke kasar ne za su yi rainon wadannan sabbin jami'o'in har zuwa lokacin da za su iya tsaya wa da kafafunsu
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta amince da kafa sabbin jami'o'i 12 a yayin da kungiyar malaman jami'o'i ta ke cikin yajin aiki, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Duk da cewa sabbin jami'o'in masu zaman kansu ne, gwamnatin ta kuma amince da kafa sabbin jami'o'in gwamnati duk da matsalolin da jami'o'in na yanzu ke fama da shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed wanda ya yi wa FEC jawabi yayin taronsu na ranar Litinin a Abuja a madadin Ma'aikatan Ilimi ya ce tsaffin jami'o'in za su raini sabbin 12 su tsaya da kafansu, rahoton Daily Trust.
Sabbin jami'o'in da za a kafa da tsaffin jami'o'in da za su raine su
Sabbin jami'o'in da za a kafa sun hada da PEN Resource University a Gombe, Jihar Gombe, wacce Jami'ar Fasaha ta Modibo Adamawa za ta raina, Al-Ansar University Maiduguri, Jihar Borno wanda za ta samu raino daga Jami'ar Maiduguri; Margaret Lawrence University, Calilee, Jihar Delta wacce za ta samu raino daga Nnamdi Azikwe University, Awka, Jihar Anambra; Khalifa Isiyaku Rabiu University Kano, wacce Jami'ar Bayero ta Kano za ta raina.
Saura sun hada da Jami'ar Wasanni, Idumuje, Ugboko, Jihar Delta wacce Jami'ar Benin, Jihar Edo za ta raina; Baba Ahmed University Kano; da Jami'ar SAISA ta Fasaha da Kimiyan Likitanci, Sokoto, wacce Jami'ar Usmanu Danfodio ta Sokoto za ta raina.
Ministan ya kuma ce Jami'ar Birtaniya ta Najeiya, Asa, Jihar Abia za ta samu raino daga Jami'ar Port Harcourt; Peter University Achina-Onneh, Jihar Anambra, za ta samu raino daga Jami'ar Nnamdi Azikiwe, Awka; Newgate University, Minna, Jihar Niger za ta samu raino daga Jami'ar Tarayya, Minna, Jihar Niger; European University of Nigeria, Duboyi, Abuja, FCT, za ta samu raino daga Jami'ar Abuja; sai North West University, Sokoto, Sokoto State wacce Jami'ar Usmanu Danfodio za ta raina.
Lai Mohammed ya ce jami'o'in da za su yi rainon sabbin jami'oin za su rika kula da ayyuka da suka hada da 'daukan manyan ma'aikata da malamai, samar da kayan aiki da kwararru don fara kwasa-kwasai; bada taimako wurin horas da ma'aikata, saka ido kan jarrabawar dalibai; sa ido kan ingancin kayan aiki, daukan dalibai da daidaita sakamakon jarrabawa.
Yajin Aikin ASUU: Ba Za Mu Bar Titunan Abuja Ba Har Sai An Buɗe Makarantu, 'Kungiyar NANS
2023: Tambuwal da Peter Obi za su shiga labule da masu ruwa da tsaki na PDP a majalisar tarayya a yau
A bangare guda, Kungiyar Daliban Najeriya, NANS, a ranar Litinin ta cigaba da zanga-zangar ta na neman ganin an kawo karshen yakin aikin da kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, ke yi.
Da ya ke magana a yayin zanga-zangar a Abuja, shugaban NANS na kasa, Sunday Asefon, ya ce daliban a shirye suke su fito su mamaye manyan titunan Abuja, rahoton The Punch.
Ya kara da cewa daliban sun gaji kuma ba za su fasa abin da suka fara ba har zai an bude dukkan jami'o'i a kasar.
Asali: Legit.ng