Kudi na magana: Dan kwallon Najeriya Ahmad Musa ya ginawa talakawa katafariyar makaranta a Jos
- Ahmed Musa na gina wata makaranta ta kasa da kasa a garin Jos, kamar yadda kyaftin din na Super Eagles ya bayyana cewa an kusa kammala ta
- Dan wasan na Najeriya ya ci gaba da sakawa al'ummar kasar nan bayan da ya gina rukunin wasanni a birnin Kano a baya-bayan nan
- A cewar matashin mai shekaru 29, Makarantar mais una M&S International School ta kammala da 99% cikin 100% kuma za a fara aiki cikinta nan ba da jimawa ba
Kaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya ci gaba da aikin gina al’umma yayin da dan wasan mai shekaru 29 ya kashe miliyoyin kudi a gina makarantar kasa da kasa a Buruku da ke garin Jos.
Ahmed Musa dai ba zai daina ba da taimako ga masu bukata, don kuwa ya gina wata makarantar zamani a garin Jos; wani yanayi na musamman.
A cikin wani faifan bidiyo da tsohon tauraron CSKA Moscow ya yada, makarantar an gina ta ne a tsarin bene mai hawa biyu tare da bangarorin azuzuwa da dama.
Makarantar ta M&S International School, a cewar Ahmed Musa, tana cikin karamar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.
Ginin dai ana sa ran zai fara aiki a zaman karatu zangon gaba kamar yadda tsohon dan wasan na kungiyar kwallon Kano Pillars ya ce 99% cikin 100% ya tabbatar.
A wata tattaunawa ta musamman da kafar labaran wasanni ta Sports Brief, Musa ya bayyana cewa yana gina makarantar ne domin taimakawa talakawa.
Yace:
"Na sayi ginin ne don in gina makarantar kasa da kasa ga talakawa a wannan yanki."
A kwanakin baya ne Musa ya dauki nauyin daukar nauyin dalibai 100 a Kano domin samun digiri a jami’a inda a shekarar da ta gabata ya kammala cibiyar wasanni na miliyoyin nairori a Kaduna inda matasa ke cin gajiyar horarwa da baje kolin kwarewarsu.
Tsohon dan wasan na Leicester City yana daya daga cikin ’yan wasan Najeriya masu arziki idan aka yi la’akari da kadarorinsa tun da ya fara buga kwallo a titunan Jos.
Alkawarin Ahmed Musa ga 'yan Najeriya: Za mu lallasa Ghana domin shiga gasar cin kofin duniya na 2022
A wani labarin, Ahmed Musa ya bayyana cewa ‘yan wasan kwallon kafan Najeriya; Super Eagles za su yi iya kokarinsu wajen ganin sun gamsar da ‘yan Najeriya ta hanyar samo tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2022, inda ta alkawarta lallasa Ghana.
Kyaftin din na Super Eagles ya ce 'yan wasan Najeriya sun yi nadamar rashin tabuka abin a zo a gani a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Senegal ta lashe watannin baya, Sports Brief ta tattaro.
Musa da yake zantawa da tashar Youtube ta hukumar kwallon kafa ta Najeriya ya yi gargadin cewa wasan da Super Egales za ta buga tsakaninta da Black Stars zai kasance mai wahala saboda hamayyar da ke tsakanin Najeriya da Ghana.
Asali: Legit.ng