Ya isa haka: Al'ummar Plateau sun fito nuna alhininsu ga barnar 'yan bindiga
- Al'ummar Plateau sun fito don yin zanga-zanga tare da neman dauki daga gwamnatin jihar kan kisan rashin tausayi da yan bindiga ke yi masu
- Jama'ar wadanda suka fusata, sun gudanar da zanga-zangar ne a sabon gidan gwamnatin jihar a ranar Laraba, 6 ga watan Afrilu
- A yan baya-bayan nan, garuruwan yankin Bassa da ke jihar na ta fama da hare-haren miyagu, lamarin da ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi
Plateau - Gamayyar kungiyoyi daga yankin arewacin Filato, kungiyar kiristocin Nejeriya (CAN) reshen Filato da matasa da mata suka hadu a sabon gidan gwamnati don yin zanga-zanga kan kashe-kashen da aka yi a garuruwan yankin Bassa da ke jihar.
Jama'ar da suka fusata sun gudanar da zanga-zangar tasu ne a yau Laraba, 6 ga watan Afrilu, domin nuna rashin jin dadinsu a kan kisan mummuken da ake masu.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa garuruwa da dama a yankin karamar hukumar Bassa sun yi fama da munanan hare-haren yan bindiga a cikin wata guda da ya gabata.
An tabbatar da mutuwar sama da mutane 20 sannan kuma an lalata gonaki da gidaje da dama.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shugaban kungiyar matasan Irigwe na kasa, Ezekiel Peter Bini, ne ya jagoranci zanga-zangar.
Masu zanga-zangar sun yi kira ga gwamnati da ta nuna jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Yayin da yake jawabi ga masu zanga-zangar, babban sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Danladi Atu, ya basu tabbacin cewa gwamnati na aiki kan yadda za a kawo karshen kashe-kashe a yankin Irigwe da kuma kawo zaman lafiya mai dorewa a garuruwan.
Atu ya bayyana cewa Gwamna Simon Lalong ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda abun ya ritsa da su san nan ya umurci hukumomin tsaro a jihar da su mamaye yankin yayinda ake gudanar da bincike don gano wadanda suka kai harin tare da gurfanar da su, rahoton Independent.
2023: Tambuwal da Peter Obi za su shiga labule da masu ruwa da tsaki na PDP a majalisar tarayya a yau
Yan Ta'adda Sun Afka Wa Mutane a Masallaci Yayin Buɗe-Baki, Sun Kashe 3 Sun Sace Wasu Da Dama
A wani labarin, mun ji cewa a ranar Talata ‘yan bindiga sun kai farmaki masallaci inda suka afka wa mutane yayin da suke tsaka da yin buda-baki, wanda ya ja suka halaka mutane uku, Daily Trust ta ruwaito.
Daily Trust ta gano yadda ‘yan ta’addan suka isa da yawansu, har suka sace wasu da yawa a masallacin sannan suka zarce da su inda ba a sani ba.
An tattaro bayanai akan yadda lamarin ya auku a kauyen Baba Juli da ke karamar hukumar Bali a cikin Jihar Taraba.
Asali: Legit.ng