PDP a Zamfara ga tagayyararrun 'yan APC: Ku shigo PDP mu kawo ci gaba Zamfara
- Jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta gabatar da tayi mai gwabi ga ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar da ke cikin damuwa
- Nura Umar wanda ke jagorantar jam’iyyar adawa ta PDP a Zamfara ya ce jam’iyyar a shirye take ta karbi sabbin mambobi daga APC
- Sai dai ya lura cewa, dole ne su bi ka’idojin da ake bukata ga duk wanda ke son zama mamba kamar yadda jam’iyyar ta tanada
Gusau, Zamfara– Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Zamfara, ya ce a shirye yake ya karbi ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki da ke cikin halin ni-'yasu zuwa PDP cikin aminci, inji rahoton Punch.
Nura Umar wanda shi ne shugaban jam’iyyar adawa ta PDP a Zamfara ya bayyana haka ne a Gusau yayin wani taron manema labarai.
Umar ya bayyana cewa babban taron jam’iyyar APC na kasa ya nuna alamun cewa wasu ‘ya’yan jam’iyyar ba su gamsu da sakamakon zaben shugabancinta ba, kamar yadda Legit.ng ta tattaro a baya.
Ya bukaci ‘yan jam’iyyar da su ke bukatar shiga jam’iyyar ta PDP da suka tunkaro PDP su shiga, inda ya ce jam’iyyar na da shirin kawo ci gaba nan kusa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Umar ya kuma bayyana cewa daukacin kananan hukumomi 14 na jihar Zamfara da PDP ke mulki sun amince da karbar duk wani dan jam’iyyar APC da ke neman dawowa PDP.
Channels Tv ta tattaro shi yana cewa:
“Za mu karbi duk wanda ke son shiga ko dawowa PDP da gaskiya. Ya kamata mu hada hannu waje guda mu ciyar da PDP gaba a jihar Zamfara.”
Ya kuma bukaci masu son shiga PDP da su bi ka'idojin da suka dace domin shiga jam'iyyar kamar yadda dokarta ta tanadar.
Bugu da kari, Umar ya gargadi 'yan PDP da kada su yiwa jam'iyya zagon kasa ko kawo cikas ga tsarinta. Ya bayyana cewa shugabannin jam’iyyar ba za su amince da irin wannan aika-aikar ba.
Gwamnatin Zamfara ta yi gargadi game da watsa lambobin wayar Matawalle a soshiyal midiya
A wani labarin, gwamnatin Zamfara ta gargadi mazauna jihar kan amfani da lambar wayar Gwamna Bello Matawalle ba tare da izini ba, jaridar Daily Trust ta rahoto. G
argadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai ba gwamnan shawara ta musamman kan wayar da kan jama’a, Mista Zailani Bappa, a ranar Talata, 5 ga watan Afrilu.
Sanarwar ta ce: “Manufar mai girma gwamna na barin lambobin wayarsa su fita cikin al’umma shine domin saka idanu sosai kan lamuran tsaro da kuma lamuran ci gaba daga tushe.
Asali: Legit.ng