Musulmi Sun Yi Zanga-Zanga Kan Miƙa Wa Fasto Filin Sallar Idi Da Suke Amfani Da Shi Tsawon Shekaru 20 a Osun
- A'ummar musulmi a garin Osogbo, babban birnin Jihar Osun sun yi zanga-zangar lumana kan yunkurin kwace musu masallacin idi da suka shafe shekaru 20 suna salla a wurin
- Kungiyoyin musulmi da suka yi zanga-zangar sun yi ikirarin cewa ana neman a kwace musu filin sallar idi a bawa wani fasto mai suna Bukola Solomon
- Qazeem Odedeji, wani lauya da ya yi magana a madadin musulmin ya gargadi hukumar kula da kadarorin jirgin kasa da kada ta haddasa rikicin addini a jihar
Osun - Musulmi a Osogbo, babban birnin Jihar Osun, sun yi zanga-zangan lumana kan yunkurin da aka ce hukumar kula da jirgin kasa ke yi na mika wa wani fasto, Bukola Solomon, filin da musulmi suka shafe shekaru 20 suna sallar Idi.
Da ya ke magana a madadin hadakar kungiyoyin musulmin na Osun a filin sallar idin da ke Oke Onitea, Osogbo, Qazeem Odedeji, wani lauya, ya ce musulmi za su cigaba da amfani da filin don sallar idi, rahoton Daily Trust.
Kwace mana masallacin idin zai iya janyo rikicin addini, Odedeji
Ya gargadi hukumar kula da kadarorin jiragen kasan kan haddasa rikicin addini tsakanin musulmi da kirista a jihar.
Odedeji ya ce an ba wa musulmi filin ne a shekarar 2015 domin su rika yin sallar idi.
Ya ce wani ma'aikacin hukumar kula da kadarorin jiragen kasa, Mr Innocent Agbaji, ya kwace filin ya bawa wani fasto a baya-bayan nan.
Odedeji ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da masu kaunar zaman lafiya su gargadi Agbaji da Solomon saboda a samu zaman lafiya.
A martaninsa, Agbaji ya shaida wa Daily Trust cewa an kwace filin daga hannun wadanda aka bawa saboda rikicin.
2023: Ƙungiyar kare hakkin musulmi ta caccaki Afenifere kan goyon bayan Tinubu
A wani labarin, Kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC, ta magantu dangane da maganganun kungiyar yarabawa ta Afenifere akan zarginta na kin goyon bayan jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu dangane da burinsa na tsayawa takara a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.
A wata takarda wacce Shugaban MURIC, Ishaq Akintola ya saki ranar Talata mai taken, ‘Tinubu: MURIC Tasks Afenifere’ ya yi maganganu akan matsayar kungiyar yarabawan.
Punch ta ruwaito yadda shugaban Afenifere, Ayo Adebanjo ya ce kungiyar sa ba za ta bi bayan wani dan takarar shugaban kasa a 2023 ba har sai an sauya kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya koma tsarin karba-karba na yankuna.
Asali: Legit.ng